Nasiha

MU AMBACI ALLAH AMBATO MAI GIRMA

????

A cikin Alqur’ani Mai Girma Allah Ya kira bayin Sa a kan su Ambace Shi Ya ce:

((فَٱذْكُرُونِىٓ أَذْكُرْكُمْ وَٱشْكُرُوا۟ لِى وَلَا تَكْفُرُونِ).

“Ku ambace ni, nima na ambace ku, ku gode min ka da ku kafirce min”. (Suratul Bakarah 152)

Kuma a wata aya Ya ce:

((يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ ٱذْكُرُوا۟ ٱللَّهَ ذِكْرًا كَثِيرًا)

“Ya ku masu Imani! Ku ambaci Allah, ambata mai yawa”. (Ahzab 41)

Kuma Ya ce:

((وَٱلذَّٰكِرِينَ ٱللَّهَ كَثِيرًا وَٱلذَّٰكِرَٰتِ أَعَدَّ ٱللَّهُ لَهُم مَّغْفِرَةً وَأَجْرًا عَظِيمًا)).

“Da mãsu ambaton Allah da yawa maza da mãsu ambatonsa mãtã, Allah Ya yi musu tattalin wata Gãfara da wani sakamako mai girma.” (Ahzab 34)

Manzon Allah (SAWW) ya ce: “In ba ku labarin fiyayyen aikin ku wanda ya fi tsarki a wajen Mamallakin ku, ya fi ɗaga darajar ku, ya fiye muku ciyar da dinare da azurfa, kuma ya fiye muku ku yi karo da abokan gabar ku, ku sare su su sare ku? Sai suka ce eh, sai ya ce shi ne ambaton Allah.” (Tirmizi da Ibn Majah)

Allah Ta’ala Yana faɗa a Hadisin Qudsi Ya ce: “Ina nan yanda bawana ya ke zato na, ina tare da bawana idan yana ambato na. Idan ya ambace ni a cikin ransa, nima sai in ambace shi a cikin raina, idan ya ambace ni a cikin taron jama’a sai in ambace shi a cikin taron jama’ar da suka fi na shi alkhairi. Idan ya kusanto ni da ibada gwargwadon taɗi ɗaya, sai in kusanto zuwa gare shi da tsahon zira’I ɗaya, idan ya kusanto ni da ibada tsahon zira’I ɗaya, sai in kusanto gare shi da bashi lada tsahon kamu ɗaya. Idan ya zo mun yana tafiya a cikin ibada, sai in zo masa da gaggawa wajen bashi sakamako”. (Bukhari da Muslim)

Wani mutum ya ce wa Manzon Allah (SAWW) ayyukan shari’ar musulunci sun yi min yawa, faɗa mun abun da zan riƙe in ta yi. Sai Annabi ya ce: “Ka da harshen ka ya daina ambaton Allah ko da yaushe.” (Bukhari da Muslim)

Kuma Annabi (SAW) ya ce: “Wanda duk ya zauna a wani mazauni bai ambaci Allah ba a cikinsa zai zame masa dana sani, haka nan wanda ya kwanta a wani makwanci bai ambaci Allah a cikinsa ba zai zame masa dana sani.” (Abu Dawud).

See also  Abin da ya kamata ku sani kan daren Laylatul Qadr

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button