Tambayoyi a Musulunci

SHARUDAN YIWA MARA LAFIYA OPERATION A ASIBITITambaya
Assalamu Alaikum. Malam ni likita ne ina aiki a asibiti, idan mara lafiya ya ki yarda ayi masa operation, makusantansa suka ki sanya a hannu a takardar shin ya haltta mu yi masa ko ba da izninsa ba ?!

Amsa
Wa alaikum assalam, ya halatta a yiwa mara lafiya operation ko ba da izninsa ba, idan aka samu sharuda guda biyu:

1. Idan aka ji tsoran zai halaka, in ba a yi masa ba a lokacin.
2. Idan ya zama cutar mai fantsama ce, ta yadda in ya zauna da ita za ta yadu a cikin mutane.

Don neman Karin bayani duba littafin malaminmu:
Sheikh Muhammad Muktar Ashshankidi
أحكام الجراحة الطبية
Allah ne mafi Sani

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
03/10/2022

See also  ZAN IYA YIWA DAN SHI'A SALLAMA ?

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button