RamadanTambayoyi a Musulunci

BANA SO NA SHA AZUMI, KO ZAN IYA SHAN MAGANIN HANA HAILA?



Tambaya:
Allah ya gafarta Malam, Azumi ya zo ni kuma ba na son na sha ko Azumi ɗaya, to shine na sayi maganin da zai hanani yin al’ada na sha, bayan mun haɗu da ƙawata, sai take ce min wai babu kyau, shine nace mata ban yarda ba, zan tambayi Malamai, don Allah Malam a ƙara min haske.

Amsa:
To ƴar uwa, amfani da maganin da yake hana haila ya halatta, idan ya zama ba zai cutar ba, amma idan zai cutar, to ya haramta, saboda faɗin Allah: “Kuma kar ku jefa kawunanku a cikin halaka”, Suratul Baƙara, aya ta (152).
Saidai duk da cewa hakan ya halatta da sharuɗan da suka gabata, amma barinsa shi yafi, sai idan buƙatar hakan ta taso, saboda mutum ya zauna akan yadda yake ya fi masa kwanciyar hankali akan yayi abin da zai canza ɗabi’arsa, musamman ma wasu daga cikin ƙwayoyin na zamani suna dagula kwanakin haila, kamar yadda ya bayyana gare mu, sai a kiyaye.
Dima’uɗɗabi’iyya, shafi na 54.
_Allah ne mafi sani._
22-06-2015

Dr. Jamilu Yusuf Zarewa.

See also  MEYA SA ALJANU SUKE SHIGA JIKIN MUTANE ?

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button