KURAKURAN DA MUTANE KE YI WAJEN AMFANI DA NA’URAR POS WAJEN CIRE KUDI
Mutane kan yi kuskure wajen ajiye bayanan bankinsu a cikin na’urar POS.
Idan za ku yi mu’amala da na’urar POS, kada ku bayyana PIN din ku ga mai POS.
Kada kuma, bayan an gama ciniki, kada ka mayar da na’urar POS nan da nan zuwa ga ma’aikacin POS, maimakon haka sai ka rike ta har sai ta Fitar da shedar takarda (Receipt) na fitar kudin ka ko Akasin haka (Approved /Declined)
koyaushe ku tabbata kun
danna maballin “clear” akan na’urar POS kafin cire Katin ka, ba tare da danna wannan maballin CLEAR ba, masu zamba za su iya samun damar samun bayanan bankinku cikin sauƙi musamman idan sun danna lamba Wasu Lambobi, wanda hakan kan basu Damar ajiye BVN ɗin ka akan na’urar POS.”
Kuma da Zarar hakan ta Faru abun ba Daɗi.
Allah ya kiyashe mu, ya Bamu ikon Adana bayanin Bankuna na customers Din mu.
Ahmad Lawan Wangara