Tech

Menene Ad Monetization?



a yanzu Ad Monetization course ne mai zaman kansa kuma Field ne me faɗin gaske kuma yana Daga cikin manyan hanyoyin samun kuɗi a internet Sa’annan Ad Monetization ya danganta da yadda akayi anfani dashi wato a matsayin
Consultant, ko amatsayin Operator kokuma amatsayin gudanar da aikin Digital services ko Influencing Shima External ko internal.

Ad Monetization wata hanya ce daga cikin hanyoyin samun kuɗin yanar gizo ko internet ta hanyar tallata hajoji a matakin internal AD Da External Ad Wanda ya haɗar da Local AdSense kokuma Third-party Ad.

ta hanyar lura da Ad Monetization kaɗai zamu fahimci tasiri da amfanin internet a duniya wanda ba shakka Ni’ima ce ta Allah Maɗaukakin sarki.

Ad Monetization hanya ce ta amfani da wani salo da basirar da Allah yayiwa mutum domin samun kuɗaɗe ta hanyar ɗaya daga cikin Social Media Platform, ko Applications kokuma Website/Blog.

Samun kuɗi a Ad Monetization yakasu kashi kashi Wanda daga cikin su akwai

Social Media Monetization

Software/Application Monetization

Blog/Website Monetization

Wanda Suke ƙarƙashin Social media monetization sun haɗar da: Facebook Monetization, Twitter monetization, WhatsApp monetization, telegram monetization, Instagram monetization
YouTube monetization
dasauran su.

Abun lura kawai shine Monetization shine Samun kuɗi ta ɗaya daga cikin hanyoyin dana ambata a sama ko wasu hanyoyin ma na daban.

Yadda Ake samun kuɗi ta Ad Monetization; dafarko dole ne mutum ya zaɓi ɓangaren dayakeso yayi implementation na monetization ɗinsa misali blog ko YouTube kokuma Instagram ko wani Platform na daban.

Nafarko; ADVERTISEMENTS AS PRIMARY INCOME Wannan tsarin samun kuɗi ne ta hanyar jefa talla a website ɗinka, ko YouTube channel ɗinka kokuma ɗaya daga cikin social media platform ɗinka wato talla na kai tsaye Kenan da za’a iya karɓa daga kamfanin Google wato Google AdSense, kokuma wasu kamfanonin da suke bayar da tallan wannan shine ake ƙira da External Ad wato tallan da aka karɓa daga kamfanonin International.

Misalin yadda zamu fahimci wannan shine irin jaridu da suke wallafa labaran su kaɗai a online kamar irin su daily Nigerian, kokuma masu finafinai da suke ɗaurawa a YouTube channel ɗinsu duka suna karɓar tallan ne daga Google ko wasu kamfanonin na daban.

Nabiyu: ADVERTISEMENTS AS SUPPLEMENTAL INCOME wannan kuwa shine Monetization ta hanyoyi daban-daban wato samun kuɗi ta hanyar tallan dakuma samun kuɗi ta hanyar siyar da wani product na ƙashin kanku a wannan Platform ɗin kokuma koyar da wani abu da sai anbiya kafin a koya kokuma siyar da wasu articles ko digital Product da makamantansu.
Misalin wannan da zamu gane dalla dalla shine kamar Application na bankuna yawanci suna saka talla aciki ko website ɗinsu Wanda kuma ba wannan bane kaɗai hanyar samun kuɗin su.

Rabe-raben Tallace Tallacen:

1.External Ad

2.Internal Ad

3.Personal Ad

External Ad shine irin su Google AdSense, internal Ad Kuma shine wanda kai tsaye Mutum zai karɓa domin ya saka a shafin sa kokuma Social Media Handle ɗinsa ta hanyar ƙulla wata yarjejeniya, Personal Ad kuma mutum ya tallata irin sana’ar sa ko aikin sa.

Yadda Akeyi: Samar da wani blog ko wani shafi domin a dinga yin wasu shirye-shirye da zasu janyo hankalin jama’a har a samu followers a blog ko website ko feji, kokuma sautin murya ko video a YouTube ko tiktok kokuma Instagram matakin farko na Monetization shine dole sai antara followers domin babu kamfani ko Mutum da zai saka tallan sa inda ba followers akwai strategies daban daban da’ake apply saide lokaci zuwa lokaci mu dinga ɗaukar ɗaya muna bayani.

Isma’il Aliyu Ubale
Albadar Global Agency Ltd
https://t.me/fasaharalbadar
8th January 2023

See also  Yadda zaka gane "FAKE ALERT" cikin sauƙi

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button