Tech

Maganin Barayin Waya, Da Masu Cire Maka Caji Su Saka Tasu Wayar Baka Sani Ba


Kowa yasan a halin yanzu satar waya ya zama ruwan dare a ko ina musamman jahar Kano garin bayin zazzagawa..????
Hakan yasa ya kamata mudinga kulawa da wayoyin mu sosai saboda mugun mutum zai iya sacewa kuma yaje yayi wata ta’asar da ita, hakan yasa nazo mana da wata Application daga kamfanin Google.

Kila watarana ka shiga cikin taron jama’a da yawa ko kuma cikin keke napep, kuma gashi yanzu ba kowa ake yarda dashi ba, bakasan waye yake zaune kusa dakai ba ga wayarka a cikin aljihun ka, to abinda zakayi shine kafin ka sakata cikin Aljihun ka zaka shiga cikin wannan application da zanyi bayani yanzu, ka seta application din sannan ka sanya wayarka cikin aljihun ka duk wanda yakai hannu yana ciro ta zata fara fitar da sautin Jiniyar Yansanda ko kuma duk sautin da ka saka mata kuma da karfi, bazata tsaya ba har sai ka karbi wayar ka cire a Password.

Kila kuma ka kwanta bacci ne kana tsaron a shigo a dauki wayar, shima zaka iya seta application din ka ajiye wayar a kusa dakai duk wanda zai taba ta sai tayi maka kara kuma bazata tsaya ba sai ka cire Password dinta.

Amfanin wannan Application ba anan kadai ya tsaya ba, akwai lokutta da dama da zaka saka cajin waya cikin falo dinku kawai sai kaninka ya lallabo ya cire wayarka ya saka tashi, batareda ka sani ba, to wannan application zata baka damar da zaran ka saka caji ana cire maka cajin wayar zata dinga ihu tana kara har sai kaji, kaga sai kazo ka duba kagani waye ya cire maka caji.

Idan kana bukatar wannan Application kaje Playstore ka rubuta “Pocket Sense-Theft Alarm App” ko kabi wannan Link din ka dauko ta kai tsaye:????

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.miragestacks.pocketsense

Allah Yataimaka ????

See also  KO KASAN RABE-RABEN LOGO DA MUKE DASU?

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button