Tambayoyi a Musulunci

MAI TAKABA, ZA TA IYA FITA AIKIN GWAMNATI?



Tambaya
Assalamu alaikm mal inada tambaya mace ce mijnta ya rasu kuma takasance tana aikin gomnati shin zata iya fita a lokacin da take takaba?
Amsa:
Wa’alaiku mussalam warahmatullah, a zahirin maganar malamai, mai takaba ba za ta je aikin gwamnati ba, tun da bai halatta mai takaba ta fita ba sai lokacin tsananin lalura, aikin gwamnati ba ko yaushe zai zama lalura ba, tun za’a iya ba ta hutu, in har ta nema, in tana da yadda zata cı abinci ya wajaba ta amshi hutu, ko da babu albashi. Saboda bin sharia shi ne zaman lafiya, duk wanda ya kiyaye Allah, to shi ma zai kiyaye shi, duk wanda ya yi hakuri Allah hakurkurtar da shi.

Amma idan ta rasa yadda zatayi ta cı abinci sai ta hanyar aikinta, to ya halatta ta yi da rana kawai, saboda Annabi ﷺ ya halattawa matan shahidai a zamaninsa, zama a gidan daya dağa cikinsu domin hira da debe kewa da rana, lokacin da suka takuru da zaman kadaici, duk da ya wajabta musu komawa gidansu in dare ya yi, Kamar yadda Baihaki ya rawaito, wannan sai ya nuna lalura tana halattawa mai takaba fita da rana, kamar yadda Ibnu-khudaama ya ambata a littafinsa na Mugni 8/130.

Duk da cewa wasu malaman Hadisin sun raunana hadisin Baihaki da ya gabata, saidai an samu kwatankwacinsa daga maganar Abdullahi dan Mas’ud da Abdullahi dan Umar, Allah ya kara musu yarda, maganar Sahabi hujja ce, in har ba’a samu wani sahabin ya saba maşa ba, kamar yadda yake a ilimin Usulul-fiqh.

Allah ne mafi sani.

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.

See also  HUKUNCIN WANDA YA SAKI MATARSA A CIKIN MAYE

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button