TarihiTarihin Sayyidina Umar

TARIHIN SAYYADINA UMAR IBN KHAƊƊABI RALIYALLAHU ANHU KASHI NA BIYARYadda Sayyadina Umar (RA) Yake Naɗa Muƙamai

Babban abin da Umar yake kula da shi a wajen naɗa shugaba shi ne ƙwarewarsa a irin aikin da ake buƙata. Da yawa Umar ya kan naɗa mutum a kan wani muƙami ya bar wasu waɗanda sun fi shi daraja saboda la’akari da iyawarsa ga wannan aiki fiye da su. Ya kan gwada mutum lokaci mai tsawo kafin ya ba shi muƙami kamar yadda ya tsayar da Ahnafu ɗan Ƙaisu tsawon shekara guda a Madina, sannan ya ce masa, na jarabta ka na lura da alheri a zahirinka, kuma ina fatar baɗininka ya kasance haka. Sannan ya yi masa wa’azi, ya naɗa shi gwamna.

Wani abin da zai bayyana mana ma’aunin da Umar ke gane wanda ya cancanci muƙami da shi, shi ne, labarin yadda ya naɗa Shuraihu a matsayin alƙali.

Ga yadda labarin ya ke:

Watarana halifa Umar ya ɗauki hayar doki daga wani talaka, ya kuma yi masa sharaɗin cewa, su biyu ne zasu hau dokin da shi da wani amininsa. Ga alama wannan dokin bai yi ƙwarin da zai ɗauki ɗawainiyar Umar tare da abokinsa ba. Amma duk da haka wannan bawan Allah ya amince, wataƙila don ganin Sarkin Musulmi zai yi amfani da shi. Kuma ko ba komai idan dokin ya samu matsala Umar mai iya Bashi Wani ne. To, amma hasashen wannan bawan Allah sai bai zamo dai dai ba, domin kuwa a lokacin da dokin ya kasa Umar ya umurce shi ne da ya haƙura ya ɗauki kayansa. Amma sai shi kuma ya ce bai yarda ba sai an bashi diyyar raunana masa abin hawa da aka yi. Da suka kasa cimma yarjejeniya sai Sarkin Musulmi Umar ya neme shi da ya samar da wanda zai yi hukunci a tsakaninsu. A nan ne wannan bawan Allah ya ba shi sunan Shuraihu, wanda ya ke ba sahabi ba ne amma yana daga cikin malamai masu basira. Shuraihu kuwa bayan da ya gudanar da bincike kan mas’alar sai ya yi hukunci da cewa, dole ne Sarkin Musulmi ya biya talakka ɓarnar da ya yi masa. Dubin irin ƙwararan matakan da Shuraihu ya ɗauka na bincike da yadda ya yi ƙarfin halin ba Sarkin Musulmi rashin gaskiya su suka sa nan take Umar ya naɗa shi alƙali. Sai Shuraihu ya kasance shi ne naɗaɗɗen alƙali na farko a tarihin musulunci.

Umar ya kan shawarci mutane game da wanda za a ba muƙami. Kuma a zamaninsa duk gwamnan da aka naɗa sai an ba shi rubutacciyar takarda da sa hannun Sarkin Musulmi a kanta wadda kuma ta ƙunshi sharuɗɗan wannan aiki da aka ɗora masa. Ya kan halartar da jama’a don su yi shaida kamar irin tsarin rantsarwar da ake yi a gaban jama’a a wannan zamani.

A koda yaushe Umar ya kan zaɓar ma mutane shugaba daga cikinsu. Ba ya ɗora baƙauye a kan ‘yan birni saboda rashin dacewar yanayinsu da al’adunsu da tunaninsu. Ya kan zaɓi masu ilmi don sukarantar da jama’a. Tausayi shi ma sharaɗi ne kafin mutum ya cancanci shugabanci a zamaninsa. Don haka, ya fasa naɗa wani mutum daga ƙabilar Banu Sulaim a kan ya ce shi bai taɓa sunbantar ‘ya’yansa ba, Umar ya ce, ba ka da jinƙai ke nan, ba za mu shugabantar da kai a kan jama’a ba.

Umar ya hana duk gwamnoninsa yin kasuwanci ko wane iri don gudun su nemi wani sassauci ko a yi musu rangwame don la’akari da muƙaminsu sai raini ko jin nauyi ya shiga tsakaninsu da talakawansu, abin da zai iya hana zartar da adalci a wajen hukunci. A kai a kai kuma ya kan rubuta wasiƙu na faɗakarwa da jan kunne zuwa gare su don su zamo masu amana da gaskiya da yin adalci a cikin aikinsu.

See also  Hoton 2Pac A Lokacin Yana Dan Karami.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button