NasihaRamadan

Abin da ya kamata ku sani kan daren Laylatul Qadr



Nabeela Mukhtar Uba ✍️

Laylatul Qadr, dare ne mai matuƙar muhimmanci ga dukkan Musulmi. A wannan dare ne Musulmai suka yi imani da cewa Allah (SWT) Ya fara saukar da Al-Qur’ani mai tsarki ga Annabi Muhammad (SAWW).

Dare ne wanda Allah Ya tara albarka mai yawa a cikinsa, duk wanda ya samu dacewa da shi, ya samu alheri mai yawa, kamar yadda Allah Ya ambata a cikin sura guda mai suna Suratul Qadri.

Ga bayanin malamai kan abubuwan da mutum ya kamata ya sani game da daren Lailatul Qadr, da kuma lokutan da ya kamata a nemi wannan dare. Malaman addinin Musulunci sun ce ana dacewa da wannan dare ne mai falala a cikin ranakun goman ƙarshe na watan Ramadana.

Daren yana ƙunshe da aminci da albarka mai ɗumbin yawa, tun daga faɗuwar rana har fitowar alfijir kamar yadda Mallam Muhammad Albani Misau, limamin Masallacin Juma’a na Babbar Sakandiren Misau a jihar Bauchi ya bayyana.

Ya ce “Alherin da ke cikin daren ya fi na wata dubu, shekara 84 kenan da watanni. “Ya ruwaito Annabi Muhammadu na cewa “Duk wanda ya yi tsayuwar daren Laylatul Qadr yana mai imani da neman lada, an gafarta ma sa abin da ya gabata na zunubansa – kamar yadda Bukhari da Muslim suka ambata”.

Shi kuwa Sheikh Khalifa Muhammadul Mashhoud, malamin addinin Islama a Najeriya, cikin hirarsa da BBC ya kafa hujja da abin da Shehu Aliyu Mai Mu’utasar ke cewa “Laylatul Qadr magana uku ce.” “Ko dai tana cikin shekara ko tana cikin watan Ramadan ko goman tsakiya,” in ji shi. Sai dai ya ce akwai waɗanda suka ce yana cikin goman ƙarshe – daren 27 bisa dalilin cewa Allah Ya ambaci Laylatul Qadr sau uku cikin Al Qur’ani.

Kuma kowane Laylatul Qadr ɗaya yana da harafi tara ne, tara sau uku zai bayar da 27 – a kan wannan suka kafa dalili cewa Laylatul Qadr yana cikin daren 27, a cewar Sheikh Mashhoud.

A wane dare ake dacewa da Laylatul Qadr?

An samu bayanai masu yawa da ba su tantance ainihin wannan dare mai albarka ba. Mallam Albani Misau ya ce wannan ne ya sa wata rana Manzon Allah ya fito zai faɗa wa Sahabbai ainihin daren, sai ya samu suna jayayya a kai, sai Allah ya ɗauke ilmin abin kamar yadda yake a ruwayar Imamu Muslim.

Ya ce hadisai da dama sun yi bayani kan wannan daren – akwai hadisin Nana Aisha (RA) da ya ce Manzon Allah ya ce: “Ku canki daren Laylatul Qadri a cikin mara ta goman ƙarshen na watan Ramadan. ”Sannan hadisin Abi Sa’id Alkhudri (RA) ya ƙara cewa Manzon Allah ya ce: “Ku nemi daren a goman ƙarshe.”

Malamin ya ce mara wato wutiri shi ne daren 21, 23, 25, 27, da 29. A ruwayar Imam Muslim kuma, “Ku nemi daren a tsakanin 29 ko 27 ko 25”.

Ya ƙara da cewa a zamanin Annabi, an taɓa dacewa da daren a 27, kamar yadda nassin hadisi ya tabbar da haka da kuma daren 21.

Abin da ya kamata Musulmi ya yi a daren

Ana son a ƙara himma da ayyukan ibada da aka saba yi na yau da kullum, ta hanyar salloli da karatun Al-Qur’ani da kyauta da sadaka da zikiri da addu’o’i. A irin wannan lokaci malamai sun ce haka Annabi (SAW) ya yi har ma ya tayar da iyalansa don su yi ibada kuma su samu albarka.

Malam Albani Misau ya ƙara da cewa akwai lokacin da Nana Aisha ta tambayi Manzon Allah irin addu’ar da za ta riƙa yi, idan ta dace da wannan daren, sai ya ce mata: “Ki ce: Ya Ubangji, lallai Kai mai yafewa ne, Kana son yafiya, Ka yafe mini.”

A cewar Sheikh Khalifa Mashshoud, akwai ɗabi’un da ake son Musulmi ya siffantu da su a wannan dare su ne ɗabi’u masu kyau, ba a samu mutum yana zage-zage ko alfahasha ba.

“Domin lokacin da yake azumi, har lokacin shan ruwa, mai azumi yana da farin ciki guda biyu – lokacin shan ruwa da lokacin haɗuwa da Ubangiji – ba ka samun farin cikin nan sai ka ɗabi’antu da ɗabi’u masu kyau cikin watan mai albarka,” in ji shi.

Hikimar ɓoye daren…

Babbar hikimar da ke cikin ɓoye wannan dare ita ce a yi ta ayyukan ibada a cikin kowane dare, ba tare da kasala ko lalaci ba. Tun farko, watan Ramadana yana ɗauke da tarin albarka har zuwa ƙarshensa, wannan ya sa Annabi na cewa: “Lallai hakan (boye daren) zai zama alkhairi ne a gare ku.” kamar yadda yake a hadisin Bukhari.

Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, fitaccen malamin addinin Musulunci a Kano ya ce “wataƙila daren da za ka tsallake yau, wataƙila shi ne daren Laylatul Qadr,”

“Ka ga hikimar idan ka raya dararen nan guda 10 da ibada, a ciki dai ɗayansu, tabbas daren Laylatul Qadr ne.” in ji Sheikh Daurawa.

Alamomin daren Laylatul Qadr

Sheikh Daurawa ya ce akwai alamomi da yawa da ake iya gane daren.

Ya ce abin da ya tabbata daga Annabi game da alamomin akwai “Idan ana sanyi mai tsanani a lokacin, za ka ga daren ba shi da sanyi sosai, idan ana tsananin zafi a lokacin, za ka ga daren ba shi da tsananin zafi, a tsaka-tsaki yake sannan washegari, idan ka kalli rana, za ka ga ta fito dau alamar babu cin zana a gefenta, alama ce ta cewa jiya daren Laylatul Qadr ya wuce.”

Ya kuma yi magana kan wasu bayanai marasa tushe da ake yi kan daren Laylatul Qadr cewa za a yaye wa mutum duniya, ka hango Ka’aba ko ba za ka ji kare ya yi haushi a ranar ba, ko jaki ba zai yi haniniya ba.

Malamin ya ce duka waɗannan maganganun ba su da wata madogara a addinin Musulunci game da wannan dare mai albarka.

See also  MU AMBACI ALLAH AMBATO MAI GIRMA

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button