Tambayoyi a Musulunci

WANDA YA SAUKE AL-QUR’ANI, BAI SAN FASSARAR SHI BA , YA YI LAIFI ?



Tambaya
Assalamu alaikum. Malam ina da tambaya na sauke Qurani amman ban san fassaransa ba, kuma ina yawan tulawa. To ya matsayin karatunnawa ?

Amsa
Wa’alaykumussalamTo ‘yar’uwa karatunki ya yi, mutukar kina yinsa ta tajwidi, ba wajibi ba ne sai kin hada haddar qur’ani da sanin fassarar shi, domin akwai daga cikin sahabbai wadanda fassarar wasu daga cikin ayoyin da suka haddace ta shigewa duhu, amma in hakan ta samu zai fi kyau, saboda hakan ita ce hanyar wasu daga cikin sahabban Annabi s.a.w, An rawaito wasu daga cikin magabata sun haddace qur’ani tun suna shekaru bakwai da haihuwa, zai yi wuya ace hade da fassarar suka haddace a irin wannan shekarun.
Sayyadina Umar ya karanta Aya a suratul A’amah a cikin hudubarsa an tambaye shi fassararta bai sani ba, hakan sai ya nuna yin hakan ba wajibi ba ne, amma kuma shi ne ya fi.

Allah ne mafi sani
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA

13\10\2015

See also  SHARUDAN YIWA MARA LAFIYA OPERATION A ASIBITI

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button