Nasir I. Mahuta

TUNUBU A MATSAYIN SHUGABAN KASA (PART ONE)

TUNUBU A MATSAYIN SHUGABAN KASA (PART ONE)

A kowanne lamari bar wa Allah zabi shi ne mafita kyakkyawa, domin Allah shi ne masanin abin da ke zuciyoyi kuma shi ya san abin da ya wuce da abin da zai zo. Ashe kuwa zabinsa shi ne zabin da babu da na sani a cikinsa.

A wannan shekarar ta 2023 Allah ya albarkace mu da samun shugaban da mu ke ta addu’ar samu amma mu ke barin kanmu da zabin kanmu ba tare da neman zabin Allah ba. Duk da ya ke Tunubu ya fuskanci makirci, tsana, jifa da karerayi tare da mummunar propaganda daga media, amma da ya ke mutane ke yin zabe, mulki kuma Allah ke bada shi ga wanda ya so. Yanzun dai Allah ya ba wa Bola Ahmed Tunubu mulkin Nigeria.

Tun da Allah ya ba shi to bari mu yi bayani ga me da alkairin da ke tattare da zaman Tunubu a matsayin shugaban kasa. Daga cikin alkairin akwai:


NIGERIA TA SAMU MAI HIKIMA:


Babban abin da ake so ga shugaba shi ne ya zama mai hikima, shi ya sa Annabawan Allah mafi yawansu hikima Allah ya ba su ba tarin ilimin karantawa da rubutawa ba. Domin ita hikima tana gaba da ilimi nesa ba kusa ba. Kuma hikima na bada ilimi shi ko ilimi ba ya bada hikima. Shi ya sa za ka ga kusan duk abin da aka samar da ke amfanar al’ummah masu hikima ne ke samar da shi. Mutum mai hikima Allah ya na ba shi mafita a hannunsa, ya yin da ake bukatar samun mafita akan kowace matsala to za a same ta ne a wajen masu hikima.

Babu shakka babu kokwanto Tunubu shi ne shugaban da Nigeria za ta yi mafi hikima a sanina. Allah ya albarkaci Tunubu da hikima, shi ya sa komai wahalar matsala idan Tunubu ya tunkare ta sai ka ga ya yi nasarar shawo kanta cikin sauki da sauri. Nigeria ta na fama da matsaloli da yawa misali; rashin tsaro, rashin hadin kai, rashin habbakar tattalin arziki da rashin kayan more rayuwa. Ku sanya ido ku ga yadda Tunubu zai samar da taro a cikin hikima, da yadda zai hada kan Yan Nigeria fi ye da tsammani cikin kankanan lokaci, da yadda zai gina Kasar nan tare da habbaka tattalin arzikinta. Kun san wani abun burgewa ga mutumin da Allah ya ba wa hikima, cikin sauki ya ke samun nasarar maganance matsala.
See also  MAI YA SA SHUGABANNI KE KOKARIN CIRE TALLAFIN MAI?


NIGERIA TA SAMU KWARARREN DAN KASUWA.


Idan batu ake na sanin matsalar al’ummah tare da sanin yadda za a fitar da al’ummah cikin kangi to yan kasuwa su ne kankat. Domin yan kasuwa su ne ke mu’amala da al’ummah a koda yaushe, su ka fi jin kukan al’ummah, su ka fi gane damuwarsu.

Wallahi akwai ilimi mai tarin yawa ciki kasuwanci wanda in ba dan kasuwa ba komai zurfin karatun mutum bai isa ya san shi ba. Shi ya sa kusan duk abubuwan da mu ke amfani da su na more rayuwa za ka ga Yan kasuwa ne su ka samar mana da su a kokarinsu na samun riba daga hannunmu. Bola Ahmad Tunubu Dan kasuwa ne da ya yi nasara a cikin kasuwancinsa. Allah ya hore masa sanin yadda za a habbaka tattalin arziki a aika ce ba wai a karance ba.

Kai Malam! Dan kasuwa fa daban ya ke ko a cikin garinku kuma a cikin Anguwanku. Komai lalacewar Anguwa idan Yan kasuwa su ka shigo ta za ka ga ta koma ta na habbaka. Ka san dalili? Domin a kowanne guri yan kasuwa na hango damarmaki ( upportunitites) wanda idan an yi amfani da damarmakin za a samu ci gaba.

Allah ya azurta Nigeria da arzikin da ya kamata ace mun wuce haka jin dadi. Mafi yawanmu muna tunanin ba ma jin dadi ne saboda yan siyasa na sace dukiyarmu ko? Tabbas akwai wannan ma, amma asalin dalilin shi ne saboda Allah ya ba mu shuwagannin da ba su iya sarrafa arzikin da mu ke da shi ba. Misalin shuwagannin Nigeria kamar misalin Kaza (hen) da ke kwana akan damin dawa amma har gari ya waye ba ta san tana kwana akan abincinta ba. Rashin sanin kuma ya sa ta ke kwana da yunwa kullum. Yan Nigeria muna rayuwa a saman dukiya amma Allah bai ba mu shugabanni masu Bussiness Mindset da su ka san inda za a taba kowa ya amfana da arzikin nan ba.

Ina mai tabbatar ma ku a mulkin Tunubu za ku ga habbakar tattalin arziki, domin duk inda ya kamata a taba za a taba domin tarawa kasa kudi. Za ku ga yadda za a habbaka kananun masana’antu, hatta jihohinmu na arewa Allah ya kawo shugaban da ya san yadda ake sarrafa arziki domin a samu arziki.

A daidai wannan gaba, akwai bukatar mu bayani game da yadda ilimin sanin kasuwancin Tunubu zai amfani Nigeria tare da habbaka tattalin arzikinta da zamanantar da kasar. Don kada rubutu ya yi yawa, mu hadu a rubutu na gaba.

See also  KAMANCECENIYAR CRYPTOCURRENCY DA ZINARE.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button