Tambayoyi a Musulunci

MAGANIN DAMUWA DA BAKIN CIKI !

Tambaya
Assalamu alaikum warahmatullah, Sheikh barka da kokari Allah yasa ka da alheri, tambaya, me yake sa yawan bacin rai ga mutum musamman ga mace, sannan meye mafita ?

Amsa
Wa alaikum assalam,
Daga cikin abubuwan da suke jawo baccin Rai akwai :

  1. Zunubai- saboda duk mai aikata su, zai samu kunci a rayuwar shi, Kamar yadda Ibnulkayyim ya fada a littafinsa Adda’u waddawa’u!
  2. Tunawa da mummunan abin da ya gabata ko kuma fargabar abin da zai faru nan gaba.
  3. Yawan burace-buracen duniya.
  4. Yawaita alaka da mutane, saboda duk wanda alakokinsa suka Yi yawa, to masu binsa bashin nauye-nauye za su yawaita .
  5. Rashin yafiya da niyyar daukar fansa.

Yawaita Istigfari, da cikakken dogaro ga Allah, da kuma takaita Mu’amala da mutane yana karanta damuwa, daga cikin addu’o’in da ake karantawa saboda yaye damuwa akwai:
لا إله إلا أنت سبحانك إني كنت
من الظالمين
Allah ne mafi Sani

Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

26/06/2020

See also  YA YI BUDA BAKI DA JIMA'I !

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button