Tambayoyi a Musulunci

INA RUBUTAWA DALIBAI WAEC, MENENE MATSAYINA ?



Tambaya :
Assalamu alaikum mallam shin ya matsayi na ya ke ? Ina taimakawa wadanda suka dade da gama makarantar sakandare wajen rubuta waec neco etc, kasancewar ba za su iya ba, ko kuma wadanda ba su samu backgorund mai kyau ba a sakandarensu, to shin mallam hakan da matsala?

Amsa:
To malam rubutawa wani jarrabawa zai shiga cikin algus din da Allah ya haramta, domin za’a baiwa wani aikin da wani ya yi, ba tare da lalura ba, Annabi s.a.w. yana cewa a cikin hadisin Muslim mai lamba ta : 279, “Duk wanda ya yi mana algus to ba ya cikinmu”

Rubutawa wani jarrabawa yana da illoli masu dimbin yawa, daga ciki : zai sanya a samu malaman da ba su cancanta ba, sannan zai jawo a cutar da al’umma, domin yanzu idan ka rubutawa wanda yake a fannin liktanci jarrabawa, ka ga zai iya zuwa ya bada magani ko ya yi tiyata ba bisa ka’ida ba.

Sannan lalurar da mutane suke kafa hujja da ita ta cewa : dalibai da yawa ba za su shiga jami’o’i ba, in ba’a taimaka musu ta wannan hanyar ba, ba zai iya zama hujja ba a shari’ance, domin za su iya ware wasu watanni su yi karatun mutukar sun yarda da bukatar su ta shiga jami’ar, ga shi kuma barnar da take cikin rubuta musu jarrabawar ta fi maslahar shigarsu jami’a girma, saboda haka sai abin ya zama ya haramta, domin idan kana so ka gane abu haramun ne ko halal, to ka kalli barna da maslahar da take ciki, in maslaha ta fi yawa to ya zama halal, in kuma barna ta fi yawa to ya zama haram, kasancewar za’a iya samun malaman da ba su cancanta ba, yana nuna girman barnar da take ciki, ga kuma kasancewarsa dangwashe da algus din da Allah ya haramta, ga shi kuma zai jawo mutane su zama kasalallu masu ci da gumin wasu.

Allah ne ma fi sani.

25-10-2014
Amsawa : Dr Jameel Zarewa.

See also  ALLAH YA TSINEWA MAI AURAN KASHE WUTA !!!

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button