Tambayoyi a Musulunci

INA AIKI DA TAKARDUN BOGI, MEYE SHAWARA?



*Tambaya*
Assalamu alaikum, Mallam wata kanwar mu ce tayi karatu sai a final Din su suka samu matsala board da yawansu.
Mallam ta fara aiki da takardan boge, Kafin taje ta gyara nata, yanzu haka takardar (original results) din na hannu tana so a Cire wancan a file din ta ayi replacing da da shi.
Shi ne take son ji ya matsayin kudin da take amsa tunda ba da takardan Gaskiya take aiki ba, kuma shin Zata iya ci gaba da aikin Idan ansa original din a file dinta?
Don Allah Mallam a taimaka mana

Amsa
Wa alaikum assalam,
Hukuncin wannan a fili yake @ zauran Fiqhu, ai Haram ta ci karara, tun ba da hakkinta aka bata ba.

Ana daukar aiki ne akan yanayin takardun mutum da gwargwadonsu, in har aka gina aiki akan karya, to duk abin da aka samu ta hanyar haka haram aka ci.

Allah ya kare mu daga cin hakkin da ba na mu ba.

Allah ne mafi sani.

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
2/04/2017

See also  ZAMAN GULMAR SHUWAGABANNI DA 'YAN SIYASA

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button