Tambayoyi a Musulunci

BAMBANTA TSAKANIN TARANSIFA DA KUDI HANNU (CASH) YAYIN KASUWANCI!Tambaya:
Tambayoyi sun yi yawa game da ‘yan kasuwan da za a zo sayayya wajansu sai su ce in kudi hannu ne sun sayar (10,000), in kuma Taransifa ne (11,000) ko makamancin haka, shin hakan ya halatta a Musulunci ?.

Amsa ;
A zahirin nassoshin Musulunci wannan cinikayyar ta halatta, saboda bambanci ne yayin siyan kaya, ba tsakanin kudi ne da kudi ba, hadisan da suka zo kuma sun hana yin fifiko ne a canji tsakanin kudaden da suke jinsinsu daya, ba tsakanin kayan kasuwanci da kudi ba.

Malaman Fiqhu suna kawo ka’idar (ضع وتعجل) wacce ta kunshi yin ragi a cikin bashin da za a amsa kafin lokacin da aka cimma daidaito ya yi, wannan sai ya nuna lokaci yana tasiri a harkokin mu’amala.

Transifa tana iya jinkirin zuwa, ta yadda ko da dan’kasuwa yana so ya yi amfani da kudin ba zai iya ba a cikin lokaci, sannan akwai kauyuka da wuraren kasuwanci a karkara wadanda ba sa amsar Transifa sai kudi hannu, sannan akwai abin da bankuna suke cira idan aka yi Taransifa zuwa asusun banki, wani lokacin ma Transifar ba za ta zo ba sai mutum ya je banki ya bi-biya, wannan yasa Bambanta tsakanin Taransifa da kudi hannu ba zai ci karo da Sharia ba.

Wanda bai bambanta tsakanin Transfer da kudi hannu ba, ya saukakawa mutane, ya kyautata kuma zai shiga addu’ar Annabi SAW “Allah Ya jikan mutumin da yake saukakawa yayin siye da kuma yayin siyarwa”.

Allah Ne Mafi Sani.

Dr. Jamilu Zarewa
10/3/2023

See also  JININ BARI BA YA HANA AZUMI

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button