Tarihi

JIRGIN SHUGABAN KASAR AMURKA NA AIRFORCE ONE.



An ƙirƙiri alamar kira ta “Air Force One” a cikin 1953, bayan da kamfanin Kira Jirage Na Lockheed Constellation Masu Kira Jiragen Boeing Ya Kera.

Shi dai wannan jirgin da ake kira “Airforce One” shine jirgin da zababben shugaban kasar Amurka, ke hawa don tafiye-tafiye a fadin duniya. Wannan jirgin yana da tsare-tsare kamar yadda ofishin shugaban kasa yake a babban birnin tarayyar kasar. Cikin jirgin yana dauke da dakuna, da ofishin shugaban kasa. Duk a cikin jirgin akwai dakin taro, da akwai yanar gizo da shugaban kasa zai iya ganawa da kowa a fadin duniya. Cikin jirgin yana dauke da wasu motocin da shugaban kasa ke hawa a duk kasar da yaje da ake kira “The Beast” guda biyu wadda basu jin harbi balle bom, sai jirgi mai saukar angulu.

An kiyasta cewar ana kashe ma wannan jirgin kimanin dallar Amurka, dubu dari biyu da shida, da dari uku da hamsin $206,350 dai-dai da naira milliyan arba’in da daya da dubu dari biyu da saba’in 41,270,000. A duk awa daya da yayi yana kunne. Yanzu haka dai an sake bada sabuwar kwangilar kera wani sabon jirgin, don ana ganin wannan ya tsufa. Wannan jirgin na daya daga cikin jiragen da aka fi kashe ma kudi a fadin duniya.

Shidai jirgin an kera shine don ya dauki mutanen da basu da yawa sosai don kuwa mutane dari kawai ya ke iya dauka banda masu tukin sa da sauran ma’aikatan jirgin kamar su injiniyoyi da sauran su. Akwai dakunan bacci da na yin taro da dakin girki duk a ciki.

Dakin Bacci

Tabbas babban jirgi ne don kuwa hadda wurin rumtsawa akwai idan an gaji. Akwai wani sashe da aka ware don masu son yin bacci.

Dakin taro:

Akwai dakin taro a cikin jirgin da ake kira John F. Kennedy. Idan akwai abubuwan da za’a tattauna a cikin jirgin, akwai dakin taro.

Ofisoshi:

Akwai ofisoshi a cikin jirgin. Akwai ofisoshin sojoji da sauran jami’an tsaron da shugaban kasar yake tafiya dasu. Akwai ofisosin yan jarida da dai sauran su.

Wurin hutawa:

Wurin hutawa kuma a cikin jirgin shine inda ake hutawa idan an gaji. Ko shakka babu shugaban kasar Amurka yana aiki sosai ba dare-ba-rana. To kam dole ne ya gaji kuma ya bukaci hutu.

Wurin shakatawa:

Duk baya da watannan kayan alatun da ke akwai a jirgin, akwai kuma wurin shakatawa. Akwai inda mutum zai kalli talabishin ko yayi anfani da yanar gizo-gizo kai harma da wasanni musamman don Amfanin kananan yaran da ake tafiya da su.

ABINCI:

A cikin Airforce one Akwai Abincin Da Mutane 200 Zasuci Dare Da Rana Tsahon Wata 6.

Menene farashin Air Force One?

Ofishin Ba da Lamuni na Gwamnatin Amirka ya ƙiyasta jimlar kuɗin a dala biliyan 3.2.

BANGAREN TSARO KUWA.

Jirgin na iya zama a sama na kwanaki, kuma an ƙera shi don jure bugu daga fashewar nukiliya.

Za ku iya bin diddigin Air Force One?

A cewar Flight Aware, Hukumar ta FAA ba ta samar da bayanan tashin jiragen soji – ciki har da Air Force One – ga gidajen yanar gizon jama’a kuma za su toshe ikon bin diddigin Tashin Jirgin.

Jirgin na yanzu yana kunshe da jiragen Boeing 747 guda biyu da aka gyara na musamman, wanda Shugaba George HW Bush ya fara amfani da Su a shekarar 1990. Jiragen biyu sun dauki kowane shugaban kasa tun daga lokacin .

Kathryn Krupnik da Eleanor Watson na CBS News sun ba da gudummawa ga wannan rahoton Da na Rubuta.

See also  Ina Kogon Masu Barci Bakwai yake (Ashabul Kahfi ) كهف الرقيم ?

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button