Tarihi

TARIHIN KASAR BRUNEI ???????? DA TARIHIN SARKIN BRUNEI SARKI HAJI HASSANAL BOLKIAHBurunai Daula ce da ke nahiyar Asiya da ke bin tafarkin shari’a irin ta musulunci. Tana ɗaya daga cikin ƙasashen duniya da talakawanta ke rayuwa cikin wadata da jin daɗi. Ita dai ƙasar Burunai wadda ake wa laƙabi da wata cibiya ta zaman lafiya, da kuma ke kusa da gaɓar ruwan kudanci nahiyar Asiya na maƙotaka da jihar Sarawak ta kasar Malasiya, hasali ma dai garin Limbang da ke cikin jihar ta Saraka ne ya raba ƙasar ta Burunai gida biyu. Kusan a iya cewa ita kaɗai ce ƙasa mai cin gashin kanta da ke kan tsubirin Borneo baya ga wani yanki na Malaysia ???????? da kuma Indonesia ????????.

Bisa ga ƙididdigar da aka yi a watan yulin shekarar 2010 ƙasar Burunai na da yawan jama’ar da basu wuce dubu ɗari hudu ba. Tarihi ya nuna cewar wannan ƙasa ta Burunai ta girku ne a cikin ƙarni na bakwai a lokacin ta ke ƙarkashin daular Srivijaya; ko da shi ke daga bisani ta koma ƙarƙashin daular Majapahit. Ita ma dai Burtaniya ta taɓa yi wannan ƙasa ta Burunai mulkin mallaka inda ta bata yancin cin gashin kanta a ranar ɗaya ga watan janairun shekarar 1984.

A shekarar 2011 ne ƙasar ta samu shiga cikin ƙungiyar ƙasashe rainon Ingila wato Commonwealth of Nations, sannan ta samu gurbi a ƙasashen da ke da kujera a cikin Majalisa Ɗinkin Duniya a ranar 21 ga watan Satumbar shekarar ta 1984.

Islama ne addinin gwamnati da kuma ‘yan Burunai

Kusan galibin al’ummar ƙasar Burunai mabiya addinin Islama ne. Magabanta wannan ƙasa sun yi gwagwarmaya ta tsawon lokaci wajen girka addinin na musulunci a ƙasar inda hakar su ta cimma ruwa a cikin ƙarni na 16 har ma aka samu nasarar gina wani katafaren masallaci. kasar dai a halin yanzu na karkashin jagorancin sarkin gargajiya wanda ake kira da Sultan Haji Hassanal Bolkiah Mu’izzaddin Waddaulah wanda ke jagorancin ƙasar bisa tafarkin addinin musulunci, duk da dai akwai tsari na sharia irin ta nasara a kasa, amma shariar musulunci ta fi karfi.

An kaddamar da shari’ar musulinci a Brunei 2014

Sarkin Brunei ya kaddamar da shari’ar musulinci a kasar ciki har da hukuncin yanke hannu da jefe mutum idan ya yi laifi mai tsauri. Sabuwar dokar dai ta fara aiki ne a 30 Ga WatanAfrilu 2014, kuma za ta hada da daure mutum ko cin tararsa idan ya aikata laifukan da suka hada da yin dabi’un da ba su dace ba da kin halartar sallar Juma’a. Haka kuma za a yi hukuncin da ya hada da yin bulala da yanke hannu idan mutum ya yi sata, da kuma rajamu idan mutum ya yi zina ko luwadi da madigo.

Sarki Haji Hassanal Bolkiah yana daya daga cikin mafiya arziki a duniya, kuma ya ce dokokin Allah su suka fi dacewa da dan adam. Masu kare hakkin dan adam sun soki lamirinsa.

Tarihin sarkin Bolkiah na daular Burunai

Hassanal Bolkiah ibni Omar Ali Saifuddien III shi ne sarki na 29 kuma na yanzu kuma Yang di-Pertuan na Brunei tun daga 1967 kuma Firayim Minista na Brunei tun bayan samun ‘yancin kai daga Burtaniya a 1984. Yana daya daga cikin sarautu na karshe a duniya.

Sultan Hassanal Bolkiah dan shekaru 76 da haihuwa An haifi Sarkin ne a ranar 15 ga Yuli 1946, a Istana Darussalam, cikin Garin Brunei (wanda ake kira Bandar Seri Begawan ) Sarkin wanda ya ke cikin jerin attajirai a duniya shi ne sarki na 28 a jerin sarakunan wannan ƙasa, Ya hau kan karagar mulkin ƙasar ne a shekara ta 1964 bayan da mahaifinsa Sultan Omar Ali ya yi murabus daga gadon mulki don kashin kansa. Sultan Hassanal Bolkia dai ya yi wani ɓangaren karatunsa a Kuala Lumpur na ƙasar Malasiya inda daga bisani ya koma gida Burunai don ci gaba da neman ilimi. A shekara ta 1967 ya hallarci makarantar sojoji ta Royal Military Academy da ke Sandhurst ta ƙasar Burtaniya. Sai dai a cikin wannan shekara ya jingine karatun na sa inda aka nada shi sarki.

Wanene ke da motoci 7000 a duniya?

Sultan na 29 na Brunei

Tarin motocin Sultan na Brunei na 29 shine mafi girman tarin motoci masu zaman kansu a duniya, wanda ya ƙunshi kusan motoci 7,000, waɗanda aka ƙiyasta ƙimar haɗin kai sama da dalar Amurka biliyan 5.

Shin Sultan na Brunei shine mafi arziki?

Sarkin ya kasance cikin masu hannu da shuni a duniya . A shekara ta 2008, Forbes ta kiyasta yawan dukiyar sarkin da ta kai dalar Amurka biliyan 20. Bayan rasuwar Sarauniya Elizabeth ta biyu a Wannan shekarar 2022, Sultan a halin yanzu shine sarki mafi dadewa a duniya a yanzu

Wanene sarkin da yafi kowa arziki?

Ya taba zama mutumin da ya fi kowa arziki a duniya kuma a halin yanzu yana da arzikin da aka kiyasta kusan dalar Amurka biliyan 28. Sultan na Brunei, Hassanal Bolkiah , shi ne kuma firaministan kasar.

Tattalin arziki da kuma Zamantakewar ‘yan Burunai

Allah ya albarkanci ƙasar Burunai da ɗanyen mai da iskar Gas mai yawan gaske wanda ƙasar ta fi ta’allaka kansu don samun kuɗin shiga. Hasali ma dai tun lokacin da aka gano arzikin na ƙarƙashin ƙasa ne, tattalin arzikinsu ya samu haɓaka matuƙa gaya. A ‘yan shekarun nan ƙasar ta yi bakin koƙarinta wajen rage dogaro da man fetur da iskar gas, hakan kuwa baya rasa nasaba da rashin tabbas na farashin ɗanyen mai a duniya da ma dai ƙoƙarin mahukuntan ƙasar na ganin al’ummarta na cigaba da rayuwa kyakkyawan yanayi ba tare da fuskankantar matsi na talauci ba.

Bisa ga irin binciken na gudanar mafi ƙarancin abinda ɗan ƙasar Burunai ke samu a matsayin albashi ko tallafi musamman ga waɗanda ke da wata naƙasa da ba zata iya barinsu su yi aiki ba shi ne dalar Amurka 500, kwatankwacin Naira dubu 214,305.00 kenan. Bisa wannan tsarin da ake da shi ne a ƙasar, ya sa masana tattalin arziki ke ganin cewar da wuya a ce an samu talaka a ƙasar duba da yadda rayuwa ta ke da sauƙi musamman ta bangaren abinci, da gidaje, da motocin haya, da tsarin kiwon lafiya, da makamantansu musamman ma dai idan aka kwatantashi da ƙasashen da ke nahiyar Afrika.

See also  Cikakken Tarihin Bola Ahmed Adekunle Tinubu (Shugaban kasar Najeriya)

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button