Tambayoyi a Musulunci

INA SO NA HADU DA MIJINA NA FARKO A ALJANNA, KO ZAI YIWU ?



Tambaya
Assalamu alaikum
Malam matar da mijinta ya mutu, sai ta yi wani auren, shin za ta sake haduwa da na farkon a lahira, in dukkansu sun shiga aljanna, ko kuma na karshen shi ne zai zama mijinta a can ?

Amsa:
To yar’uwa malamai sun yi sabani akan wannan mas’alar zuwa zantuttuka guda uku:

1. Za ta zauna da wanda ya fi kyawawan dabi’u a duniya.
2. Za’a ba ta zabi.
3. Za ta zauna da na karshensu.

Wannan maganar ta karshe ita ce mafi inganci saboda fadin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi cewa : “Duk matar da mijinta ya mutu, ta yi aure a bayansa, to ranar lahira za ta kasance ga na karshensu” Albani ya inganta shi a Sahihu-jamiussagir a hadisi mai lamba ta: 2704.

Wannan kuma shi ne dalilin da ya hana matar Abuddarda’a aure bayan mijinta ya mutu, lokacin da Mu’awiya ya nemi ya aure ta, ta ki yarda ta aure shi, saboda tana so ta zauna da abudarda’a a lahira. duba silsilasahiha hadisi mai lamba ta: 1281.

Munawy yana cewa: “Malamai suna cewa: Wannan shi ne daya daga cikin dalilan da suka sa matayan Annabi ﷺ ba su yi aure ba bayansa, saboda Allah ya riga ya kaddara cewa: matayansa ne a aljanna” duba Faidhul-kadeer 3\151

Allah ne mafi sani.

08/02/2015.

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.

See also  MAGANIN DAMUWA DA BAKIN CIKI !

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button