Tarihi
Me ranakun Tasu’a da Ashura ke nufi ga Musulmai?
Tasu’a da Ashura’a ranaku ne da al’ummar Musulmai da Yahudawa a faɗin duniya ke girmamawa da ibada ta musamman kamar azumi.
Ranakun na kamawa ne a 9 da kuma 10 ga watan Muharram na kowace shekarar Musulunci, kuma na bana za su kama ne a ranakun Lahadi da Litinin a Najeriya – waɗanda suka yi daidai da 7 da 8 ga watan Agustan 2022.
Kazalika, wasu ƙabilu kamar Hausawa kan gudanar da wasu abubuwa na al’ada a ranar Ashura.
Haka nan, Musulmai mabiya Shi’a kan shafe ranar Ashura ta hanyoyi na musamman, inda suke kallon ranar a matsayin ta baƙin ciki saboda kashe Hussaini jikan Annabi Muhammadu (SAW) da aka yi a ranar.
Cikin wannan maƙala, mun duba muhimmanci da tarihi da abin da ake son Musulmai su yi a ranakun biyu.
Tarihin Tasu’a da Ashura.
Kalmar Tasu’a na nufin tara ga wata yayin da Ashura ke nufin goma ga wata, a cewar Wani Malamin Ahalul Sunna Imam Murtadha Muhammad Gusau, babban limamin masallacin Nagazi-uvete da ke garin Okene na Jihar Kogi a tsakiyar Najeriya.
Malamin ya ce ranakun sun samo asali ne tun lokacin da Annabi Muhammadu (SAW) ya yi hijira daga garin Makka zuwa Madina, inda ya tarar mabiya addinin Yahudanci na yin azumi a ranar 10 ga Muharram – Ashura.
Da ya tambayi dalilin da ya sa suke azumin sai suka faɗa masa cewa saboda ita ce ranar da Allah ya kuɓutar da Annabi Musa (AS) daga hannun azzalumai kuma ya halaka Fir’auna.
“Wannan dalilin ne ya sa Annabi ya ce to ai mu ne muka fi kusa da Annabi Musa, saboda haka mu ma za mu dinga yin azumi a wannan rana domin girmama shi,” in ji malam Murtadha.
Ya ci gaba da cewa: “Bayan haka ne kuma wasu sahabban (abokan) manzon Allah suka faɗa masa cewa ka sha gargaɗinmu da mu guji koyi da Yahudawa amma ga shi yanzu za mu yi koyi da su wajen yin azumin Tasu’a.
“Sai Annabi ya ce to idan Allah ya kai mu shekara mai zuwa za mu yi azumi ranar 9 sannan mu yi a 10 ga watan Muharram don mu saɓa wa Yahudawan.”
Sai dai malamin kafin shekarar ta zagayo Annabi yayi wafati. Amma duk da haka Musulami sun ɗauki yin azumi a ranakun biyu a matsayin Sunna tun da Annabi ya yi umarni da su yi.
Me ake son Musulmai su yi a ranakun?
Amsar wannan tamnbaya ta danganta ne da ɗariƙar da kowane Musulmi yake bi.
Imam Murtadha Gusau ya ce ibadar azumi ce kaɗai abin da ya tabbata a Shari’a wadda ake son Musulmai su yi a ranakun Tasu’a da Ashura.
Sai dai malam Muhammad Mashhud da ke jihar Zamfara ya bayyana abubuwa 11 da ake son Musulmi ya aiwatar a ranakun duk da cewa wasu malamai sun ce hadisin bai inganta ba. Su ne:
1, Azumi
2, Sada zumunci
3, Sallar nafila
4, Ziyaratar malami
5, Wanka
6, Shafa kan maraya saboda tausaya masa
7, Sadaƙa
8, Shafa kwalli
9, Yalwata wa iyali
10, Yanke farce
11, Karanta Suratul Iklas ( Kurhuwallahu Ahad )
Ranar Cika-Ciki – ranar farin ciki
Bisa al’ada, al’ummar Hausawa kan kira ranar Ashura da Ranar Cika-Ciki. Wasu ma kan kira watan na Muharram da watan cin jela.
Daga jin sunan an san cewa yana nufin farin ciki da ciye-ciye da yalwata wa iyali.
Iyalan Hausawa kan yi girke-girke na musamman a wannan rana sannan su aika wa maƙota domin sada zumunci – ko da yake dai al’adar ba a aiwatar da ita sosai yanzu a birane.
Sai dai Imam Murtadha Gusau ya ce wannan al’ada ce wadda ba ta da tushe a Musulunci.
Ranar baƙin ciki ga ‘yan Shi’a
Ashura rana ce ta baƙin ciki saboda tunawa da kashe imam Hussaini jikan Annabi Muhammadu Sallallahu alaihi Wasallama a garin Karbala da ke Iraƙi a yanzu.
‘Yan Shi’a kan saka baƙaƙen kaya mazansu da matansu, yara da manya, har ma su dinga duka tare da ji wa kansu ciwo duk don tunawa da kisan. Wasu kan shiga wuta su ƙona jikinsu.
Kazalika, sukan yi maci ko tattaki a kan tituna.
Abu ne sananne a shekarun baya, wasu ‘yan Shi’a kan yi tattaki – tafiya da ƙafa – daga garin Kano zuwa Zariya da ke Jihar Kaduna ta arewacin Najeriya a ranar Ashura.
Ranar farin ciki ga Nawasiba.
Imam Murtadha Gusau ya ce akwai wasu mabiya ɗariƙa da ake kira Nawasib waɗanda su kuma farin ciki da wannan kisan da aka yi wa Hussaini jikan Annabi suke yi.
“Za ka ga a wannan rana su ‘yan Nawasib murna suke, suna yanka dabbobi saboda su saɓa wa ‘yan Shi’a. Su suna murna ne da abin da ‘yan Shi’a ke baƙin ciki a kan sa,” a cewarsa.
“Sai dai duk wanda ya yi murna ko baƙin ciki a wannan rana ya saɓa wa Shari’ar Musulunci saboda babu abin da ya inganta daga Annabi Muhammad SAW a kan hakan saɓanin azumi.”