Tambayoyi a Musulunci

YADDA AKE BIYAN TSOHON BASHI !Tambaya
Salam. Ina da tambaya
Na ranci kudi fam biyu kamar shekaru (62) da suka wuce, ban biya ba.
In zan biya yanzu da haka fam biyun zan biya ko ko ya zaa yi ?

Amsa
Wa alaikum assalam
Wasu malaman sun tafi akan cewa zai biya kima ne, na kudin da ya ranta, misali Fam biyu me za ta iya siya a wancan lokacin, sai a bada kimarta a yanzu, saboda in an biya da adadinsu akwai cutarwa ga wanda ya ba da bashin, kuma yana daga cikin ka’idojin Sharia tunkude cuta gwargwadon iko.

Malaminmu Sheikh Ibnu Jibrin (Bajimin malami, mai amsa fatawa a Saudiyya) ya tafi akan cewa ana iya biyan kwatankwacinsu daga kudin da darajarsu ba ta faduwa kamar Dalar Amurka.

Allah Ne Mafi Sani

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
7/03/2023

See also  HUKUNCIN YIN SALLAR NAFILA BAYAN WUTIRI!

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button