Wasu Abubuwa Da Suka Kamata Duk Namiji Ya Sani Game Da Kan Tsinin Nonuwan Matar Ka
Ka nonuwan mata da aka fi sani da sunan nipples a turance, bangare dake jikin mace na nonuwanta da yake tattare da wasu abubuwan da ya zama dole maza su sansu.
Baya ga bangare ne da shine mafita abincin da jarirai suke sha na ruwan nono, waje ne da yake motsa akasarin sha’awar mata da zaran an taba shi, murza shi ko shan sa. A wani darasi a baya munyi bayanin abunda yasa shi nipples yake kumbura idan sha’awar mace ya motsa.
Nipples dai ka kasu kashi daban daban a jikin mata har sama da kaso 100. Halitta ne da ko wani nahiya, kabila ko zuriya suke da irin nasu kalar. Wanda maza da dama basu fahimcin hakan ba, wasu na dauka duk kan nonuwan mata iri guda ne.
Akwai matan da kannonuwansu yake da fadi, wani tsini, wani a baje wani kuma a kumbure. Wata nata da girma kamar kan babba dan yatsa, wata kuwa sai ka nemo shi da kyar akan kirjin ta.
Yana da kyau kuma maza su fahimci cewa, kan nonuwan mace na iya sauyawa daga yadda yake zuwa yanayin da mace take. Yana iya sauyawa a launi ko girma musamman idan mace tana da ciki, rama ko yin jiki.
Akwai matan da kan nonuwan su bakine wul, amma sai ya dawo fari, wata kuwa nata fari sai kuma ya sauya ya zama baki. Haka nan idan yana da kankanta yana iya kara girma.
Ba abun mamaki bane namiji yaga mace da kan nonuwa biyu a nonon ta guda.
Wannan ba wani illa bane a cewar masana kiwon lafiya, inda suka kara da cewa ma, dukkanin kan nonuwan suna iya fidda ruwan nono domin baiwa jariri. Don haka kada kaga matarka da kan nonuwa biyu a nono guda kace ka auro manya.
Sannan ana iya samun kan nonuwan mace guda biyu suna iya bambamta. Kan nonuwan hagu ya bambamta dana dama, shima masana suka ce ba matsala bane.
Suma mata ana iya samun gashi a kewaye da kan nonuwansu kamar dai yadda ake samun gashi akan nonuwan wasu matan.
Kaman yadda ake samun wasu abu masu kama da kuraje akan kaciyar wasu mazan.
Haka nan ana samun wasu kurzunu kurzunu suma kamar kuraje ne akan nonuwan wasu mata. Shi dai wannan kurajen da ake kira a trance Montgomery, bayyanansu kan nonuwan mace ba wani illa bane. Domn shi da wannan bakin kan nonuwan mace mai suna areola, suna samarwa kan nonuwan mace wani mai da laushi domin hana kan mace tsagewa ko bushewa a lokacin da take shayarwa. Don haka ba haka nan kawai Allah Ya yisu ba.
Ba duk maza bane suke da masaniyar cewa, wasa da kan nomuwan matarka a lokacin nakuda zai iya sata ta samu saukin haihuwa. Cewar masana, idan kana mulmula kan nomuwan matarka kana samar mata da sinadarin oxytocin, samar da wannan sinadarin kuma na taimakawa mace wajen haihuwa.
Ka nonuwan mace na bayyana irin yadda lafiyar ta yake. Don haka maza kuna iya fahimtar lafiyan matanku ta hanyar murza, tsotsa, sha da kuma shafan nonuwan matayenku.