Tambayoyi a Musulunci

IDAN IDI YA FADO A RANAR JUMA’A, ZA’A BAR SALLAR JUMA’A !!



Tambaya
Assalamu alaikum Dr. Barka da warhaka , idan ranar Eid ta kasance ranar jumaa zan iya zuwa eid na bar jumaa ko kuma akasin hakan ❓

Amsa
Wa alaikum assalam
Idan Idin karamar sallah ko babba ya fado ranar juma’a to akwai maganganun malamai guda uku:

1. Zai yi IDI kuma Juma’a ba za ta fadi akansa ba, saboda Juma’a wajibi ce akan kowa don haka ba za ta fadi saboda IDI ba, Wanda yake bawa wajibi ba ne, wannan ita ce maganar Malikiyya da Hanafiyya.

2.Ya halatta ga wadanda suke ‘yan Kauye su bar Juma’a, idan sun yi IDI sai su koma gida, Ba dole sai sun halarci Juma’a ba saboda hakan zai wahalar da su, tun da ba’a gari suke ba, ga shi kuma babu kuntatawa a cikin musulunci.

3. Wanda ya yi idi zai iya barin Juma’a, saboda Ibnu Majah ya rawaito hadisi daga Ibnu Umar a lamba ta: (1312) cewa: “Annabi S. A. W. ya yi rangwame idan Juma’a ta hadu da IDI a kyale sallar juma’a”

Zance na uku ya fi inganci saboda hadisi yana goya masa baya, tare da cewa, ya wajaba ga wanda bai je Juma’a ba ya yi Azahar, tun da an yi rangwame akan barin Juma’a ne saboda wahalarwa a cikin hada biyun, hakan kuma babu shi a Azahar .
Wanda yake Liman ne zai yi Juma’a saboda wadanda za su halarta, saboda fadin Annabi SAW Lokacin da yi sauki game da Juma’a “Amma mu za mu yi juma’a” Kamar yadda ya zo a riwayar Ibnu Majah wacce ta gabata.

Don neman Karin bayani duba: Mudawwanah 6/153 da kuma Al-mugni 2/105

Allah ne mafi sani.

Dr. Jamilu Zarewa
15/06/2018

See also  HUKUNCIN WANDA YA SAKI MATARSA A CIKIN MAYE

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button