RANTSUWAR MANZON ALLAH (SAWW) A KAN ABU UKU.
عَنْ أَبِي كَبْشَةَ الْأَنْمَارِيِّ رضي الله عنه
قَال َ: سَمِعْتُ رَسُولَ اللهِ ﷺ يَقُول ثَلَاثٌ أُقْسِمُ عَلَيْهِنَّ، وَأُحَدِّثُكُمْ حَدِيثًا فَاحْفَظُوهُ
Hadisi daga Abi Kabshatal- Anmãriy (RA) Yace: Naji Manzon ALLAH (SAWW) Yana cewa: Abubuwa uku ina rantsuwa da ALLAH akansu, kuma zan fada muku wata magana akansu, dan haka ku kiyaye abinda zan fada muku.
قَالَ :فَأَمَّا الثَّلَاثُ الَّتِي أُقْسِمُ عَلَيْهِن
Yace: Abubuwa uku da nake rantsuwa da ALLAH akansu sune:
NA FARKO
فَإِنَّهُ مَا نَقَّصَ مَالَ عَبْدٍ صَدَقة
Wallahi babu wata dukiyar Bãwa da zata tauye saboda sadaka. (Da Kyauta).
NA BIYU
وَلَا ظُلِمَ عَبْدٌ بِمَظْلَمَةٍ فَيَصْبِرُ عَلَيْهَا إِلَّا زَادَهُ اللهُ بِهَا عِزًّا
Wallahi babu wani Bãwa da za’a zalunce shi akan wani abu, yayi hakuri akan zaluncin da aka masa, fáce ALLAH ya Kara masa Ďaukaka a dalilin hakurinsa.
NA UKU
وَلَا يَفْتَحُ عَبْدٌ بَابَ مَسْأَلَةٍ إِلَّا فَتَحَ اللهُ لَهُ بَابَ فَقْرٍ
WALLAHI
Babu wani Bãwa da zai budewa kansa kofar roko (Maula) face sai ALLAH ya bude masa kofar talauci.
????أخرج أحمد في مسنده تحت رقم (18031)وحسنه محققو المسندوصححه ألباني????
.
TAMBIHI
Na farko:
Sadaka kyauta, taimako da dukiya, basa tauye dukiyar, domin ALLAH ya fada a cikin Alkur’ani cewa:
وما أنفقتم من شيء فهو يكلفه
Duk abinda kuka bayar na wani abu daga dukiyarku ALLAH zai maida muku da Madadinsa.
NA BIYU:
Duk wanda ya zalunceka akan dukiyarka ko Wani hakkinka, ya nemi yafiyarka, kayi hakuri saboda ALLAH tare da cewa kanada ikon daukan fansa, ALLAH zai Ďaukaka ka yaba ka fiye da abinda aka zalunce ka akan sa.
NA UKU;
Bara, maula ba abinda suke sabbabawa ma’abotansu face talauci.
Manzon ALLAH (SAWW) yace;
ومن يستعفف يعفه الله، ومن يستغني يغنيه الله، ومن يتصبر يصبره الله
Duk wanda yakãme daga rokon mutane ALLAH zai rufa asirin sa, duk wanda ya wadatu da Abinda ALLAH Ya Bashi Allah zai wadata shi, duk wanda yayi hakuri da halin da yake ciki, ALLAH zai sanya masa hakuri da nutsuwa a zuciyarsa.