Tech

KO KASAN RABE-RABEN LOGO DA MUKE DASU?

Yana da kyau ace mun sansu…

MUNA DA RABE-RABEN LOGO HAR GUDA 7, WANDA SANINSU ZAI FADADA MAKA ILIMINKA NA GRAPHIC DESIGN.

1. MONOGRAM LOGO or LETTERMARKS.

Tsarin samar da tambari ne (Logo) wanda ake gajarce sunan kamfani zuwa ba’ka’ken haruffa (Capital Letters) guda 2 ko 3. Misali: HP, CNN, IBM da wasunsu.
Wa’dannan duk suna daga cikin kamfanunnuka masu tsayin suna da sukayi amfani da tsarin monogram wajen samar da tambarinsu. wasu sukan ha’da da ‘kananan harufa wajen yin monogram logo amma a ra’ayinsu na kansu ne suke yin hakan.

monogram logo yafi cancanta ga kamfanin da yake da hanyar bun’kasa sunanshi a sanshi ko da ba’a ambaci sunanshi ba gaba ‘daya.

2. WORDMARKS or LOGOTYPE

Shima tsarin ‘kir’kirar tambari ne (Logo) wanda yake kamanceceniya da Lettermark logo, Wordmark or Logotype logo ne wanda ake samar dashi daga tsarin harufffa (Fonts) kuma ya fakaitu ne kawai akan sunan kamfani ka’dai, misali: Coca-Cola, Google, Visa da sauran irinsu. Haka kuma yana da muhimmanci sosai wajen bayyana sunan kamfani domin sunane kawai ajiki.

3- PICTORIAL MARKS or LOGO SYMBOL

Pictorial mark logo a wasu lokutan ana kiranshi da Brand Mark ko kuma Logo Symbol, ana amfani da icon ne wajen yinshi, mafi yawa wani ‘dan hoto wanda zaiyi nuni da kamfani yake akai ko kuma hoton da suke ra’ayi dan wakiltar sunan kamfaninsu, misali: Twitter logo da Apple Logo.

Pictorial Mark logo yana wakiltar sunan kamfani koda ba’a rubuta sunanshi ba, saboda ana yawan amfani dashi a wajaje da dama ba tare da sunan kamfanin
ya bayyana ba.

See also  YADDA AKE CONNECTING ANDROID XENDER DA COMPUTER

4- ABSTRACT LOGO MARKS

Abstract Logo Marks shi kuma wani bangare ne na musamman daga cikin tsarin Pictorial Logo, amma shi yana samuwa ne daga Abstract Geometric Shapes, misali: Adidas Logo, ko kuma Pepsi Logo.

Mafi yawancin Abstract Logo Marks ba’a cika samun kamanceceniya ba a tsakanin tamburansu, kasantuwar shapes dinda ake amfani dasu wajen yinshi ‘kir’kirarru ne daga tunanin dan adam.

5- MASCOTS LOGO

Mascot Logos logo ne wanda ake amfani da suffa ta zane (Illustrated Character) ana saka mashi launika sosai, sannan yana yin kama da sufar Cartoon, wasu lokutan ma yana bayar da dariya ga masu dubanshi, misali: KFC Mascot Logo, da Kool Aid Mascot.

6- THE COMBINATION MARK LOGO

Tsarin samar da logo ne wanda ya ‘kunshi Wordmark, Lettermark, Pictorial mark, Abstract mark ko kuma Mascot.

Combination Mark Logo yana samar da hoto tare da rubutu ta yadda akaso a tsarasu, daga gefe ne, ko sama ko kuma a tsakiya ko ‘kasa, misali: Lacost Logo, da Doritos Logo.

7- THE EMBLEM LOGO

The Emblem Logo tsarin ‘kir’kirar tambari ne wanda ya ‘kunshi Fonts a tsakiyar Symbols ko Icons. Zamu dangantashi da tambarin da ake yawan sakawa akan badges (baje), wasu lokutan yana bayar da sufa ta hotunan gargajiya ko masu kama da hakan. A takaice dai amfi amfani da irin wannan tsarin na logo ga makarantu, ko wasu ma’aikatu na gwamnati, misali: Harley Davidson Emblem Logo, ko Starbucks Emblem Logo.

Abu Ibrahim

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button