Nasir I. Mahuta

BAYANIN AKAN YADDA RAI YA KE .Sanin yadda RAI ya ke gaibu ne da har yanzu masana basu gano inda hakikanin rai ya ke a gangar jiki ba.

Abinda na fahimta rai ba wata tsoka ba ce da za ka gani ka taba. Rai PROGRAMING ne wanda Allah ya yi ya sanya a jikin Dan Adam. Kamar yadda computer take ba ta iya aiwatar da komai sai da Programms wanda ake yin Programming dinsu da programming languages.

Gangar jikin dan Adam HARDWARE ne yayin da tunaninsa, ransa, da feeling na sa SOFTWARE ne. Ita kuma software ba’a kallonta ballantana ka taba, amma itace masarrafin HARDWARE.

Idan kana so ka fahimci yadda rai yake to ka fahimci yadda FIRMWARE FLASH FILE ya ke a jikin waya. Da za ka sawo sabuwar waya ba zata yi aiki ba idan flash file nata ya yi corrupt. Wata ma ba za ta kawo koda haske ba har sai an dora mata sabon flash file.

Wayar kamar gangar jikin matacce ce, ba za ta yi komai ba. Rai kamar FLASH FILE ne wanda ana Install nasa a cikin waya sai kawai ta ci gaba da aiki. To kamar haka rai ya ke a cikin Dan Adam. Allah ne yayi PROGRAMING nasa kuma yayi INSTALLING na shi a jikin dan adam. Idan Allah ya turo mala’uku suka yi UNINSTALL na wannan PROGRAM din to nan take sai ka mutu ka kasa koda motsi.

Yayin da Allah ke halittar Dan Adam a cikin Mahaifiyarsa daga MANIYYI ya koma JINI daga JINI ya koma TSOKA. wannan lokacin an gama kera gangar jiki Dan Adam kenan. Amma ba zai iya komai ba sai an Busa masa rai. Busa rannan INSTALLATION ne na rai, wanda shi rannan SOFTWARE ne.

Baki, hanci, ido, kafa, zuciya, kunne da sauransu da ke jikin Dan Adam dukkaninsu HARDWARES ne. Ba za su iya yin komai ba sai idan SOFTWARES (APPLICATION) nasu na RUNNING a jikin dan adam.

PROGRAMMING LANGUAGE yare ne wanda ake umurtar gangar jikin computer da shi, yayin yin programming na computer ana amfani ne da yare wanda ta ke iya ji har ta yi abinda aka ce ta yi.

Dukkanin Halittun ALLAH yana sarrafa su ne da PROGRAMING LANGUAGE na كن فيكن (KUN-FAYAKUN)

Idan ka kalli jimlar KUN FAYAKUN a Larabce za ka iya fahimta kamar haka:

KUN FAYAKUN kalmomi biyu ne da ke kunshe da ACTION= RESULT.

KUN (كن) na mufin ‘KASANCE” FAYAKUN na nufin “SAI YA KASANCE) Ma’ana’ KUN’ ACTION domin umurni aka bada. Ita kuma FAYAKUN RESULT ne domin ita ce ke bayyana sakamakon Umurnin.

Anan zamu iya fahimtar cewa KUN-FAYAKUN kamar INPUT ne da OUTPUT: INPUT na jikin dan adam shi ne PROGRAM din da Allah sanya a gangar jikin, yayin da OUTPUT shi ne Rayuwar da gangar jikin ke yi.
________________________________________________
A wani Nazari da na yi na fahimci abubuwa guda uku:

1. Allahu ya halicci Mutane da KASA, domin su zama suna da BODY shi ya sa a halittar gangar jikin Annabi Adam Allah ya yi sane da hannayensa (wanda shi ya san yadda suke), Gangar jiki Hardware ne.

2. ALLAH ya Halicci Mala’iku a Da HASKE wanda HASKE software ne.

3. ALLAH ya Halicci ALJANAI da WUTA wanda wutar Software ce.

Kasar da aka aka halicci Mutum da ita a Turance ita ne Soil, hasken da aka halicci MALA’IKU da shi light ne, yayin da wutar da aka halicce ALJANAI da ita ELECTRICAL CURRENT ne.

Manzon ALLAH ya ce “kowanne Dan Adam yana tare da Mala’iku da Aljanai” Hakan na nufin kowanne dan adam yana tare da LIGHT FORCE and ELECTRICAL FORCE ma’ana Mala’iku da Aljanai. Shi ya sa na ce Dan Adam kamar Computer ne, computer na rayuwa ne da light and electrical current.

Haske da wuta suna da kama amma suna da bambanci, Light Force da Electrical Force suna da kama amma suna da bambanci kuma dukkaninsu ido ba ya kallon su. Mala’iku da aljannai suna da kama dukkanin su ido baya kallonsu.

Annabi ya ce “MALA’IKU ne ke sarrafa dukkanin sassan jikin dan adam” hakan na nufin Mala’ika a jikin Dan Adam kamar APPLICATION ne a cikin COMPUTER. Idan za ka dauki hoto dole ka shiga APPLICATION na CAMERA. Haka ido baya iya kallo sai APPLICATION na idon ya yi Running ma’ana sai Mala’ika da ke sarrafa idon ya sarrafa.

Shedan wanda Allah ya halitta da wuta a jikin dan adam kamar CURRENT ne a jikin computer, babu yadda za’ayi computer ta yi aiki babu current kamar yadda babu Dan Adam din da ke rayuwa da babu Aljani a jikinsa.

APPLICATIONS din da ke sarrafa jikinka wato mala’iku suna da Record na duk aikin da suka yi. A wajen Hisabi Allah zai nuna maka REPORT S da aikin da suka sarrafa jikinka ka yi.

Na fahimci ALLAH ya Halicci Dan Adam ne da sigar da zai masa biyayya ne zalla. Idan kaga dan adam ya kangarewa umurnin Allah to shedan ne. Shi ma shedan yana amfani da VIRUS ATTACK ne sai ya chanja tunanin Dan Adam kamar yadda VIRUS ke sanya MEMORY ya yi MISBEHAVE. Idan Allah ya so mutum da shiriya sai ya saka masa ANT-VIRUS da zai lalata VIRUS ATTACK da shedan ya yi wa MEMORY na Dan Adam.

Wannan misalai ne kawai da za ka fahimci yadda rai ya ke a cikin Dan Adam. Ban ce na ga bayanin a hadisi ko aya ko kuma wani littafi ba, na yi nazarin ne bisa tunanina da fahimta ta.

See also  KA GWADA WANNAN SANNAN KA BANI LABARI

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button