Tarihin Annabi Sulaiman

Tarihin Annabi Sulaiman/Suleman (AS) Kashi Na (3) Kuma Na KarsheAljanu sun yi takara da juna don faranta masa rai. Daya daga cikinsu mai suna Ifrit ta ce: “Zan kawo muku shi a cikin kiftawar ido!”

Sai Ifrit Yace da Annabi Sulaiman Daga Kanka Sama Sai Ya Daga Sai Ifrit Yace Sauke, Yana Saukewa saiga Gadon Bilqis a Gabansa Sulemanu Lallai an kammala aikin Kawo a cikin kiftawar ido. Kujerar Mulkin Annabi Suleman tana cikin Falasdinu, ita kuma masarautar Bilqis ta kasance a Yemen, Tafiyar mil dubu biyu. Wannan babbar mu’ujiza ce da ɗaya daga cikin waɗanda suke zaune tare da Annabi Sulemanu ya yi.

Lokacin da Bilqis ta isa fadar Annabi sulaiman, an tarbe ta cikin fara’a da mutuntawa.

Sai Sulemanu ya yi nuni ga Gadon da Aka Dauko na Bilqis ya tambaye ta ko gadon ta data baro a Yaman ya yi kama da wannan? Ya kalleta, A ranta ta tabbata cewa lalle gadon nata ba za ta iya zama wadda take kallo ba, kasancewar nata yana cikin fadarta; da, ta gano kamanni mai ban mamaki kuma ta amsa: Sai tace “Kamar shi ne, kuma ya yi kama da nawa ta kowace fuska.” Annabi Sulemanu ya tabbatar da cewa lallai Bilqis ta kasance mai hankali da iya diflomasiya.

Alkur’ani Yace:

TO A YAYIN DA TAZO (FADAR ANNABI SULAIMAN ) SAI AKA TAMBAYETA : KAMAR HAKA GADONKI YAKE? SAI TACE ”YANA KAMA DA SHI”. TO ILIMIN DA AKA BAMU YA DARA HAKA, KUMA DUK MUN MIKA WUYA GA ALLAH HAKIKANIN MIKAWA”.

(Kur’ani sura ta27 aya ta 42 ).

Bayan ta gane cewa gadontane na mulki, sannan ta fahimci baiwar da Annabi Sulaiman ke da ita, sai ta shiga cikin kasaitacciyar fadar tasa.

Daga nan ya gayyace ta zuwa cikin babban falo wanda aka Shifida tiles da Akayi da gilas Mai kyalli A zatonta ruwa ne, taza shiga don haka ta d’aga siket dinta sama saboda tsoron karta jike Kawai sai taji Annabi Sulaiman yace da ita:

”WANNAN AI FADA CE DA AKA GINA HANYOYIN TA DA GILASHIN KARAU “.

(Kur’ani sura ta 27 aya ta 44)

Alkur’ani ya bamu labari cewa:

“ta dauka wani ruwa ne sai ta dage halliyarta [don ta ratsa ta]. Ya ce: “Lalle ne shi, gini ne mai santsi da gilashi.” Ta ce: “Ubangijina! ( 27:44 )

Tayi mamaki, Bata taba ganin irin wadannan abubuwan ba. Bilqis ta fahimci cewa tana tare da wani mutum mai ilimi sosai wanda ba wai kawai mai mulkin babbar daula ba ne, shi ma manzon Allah ne. Ta tuba, ta bar bautar rana, ta yarda da imani da Allah, kuma ta nemi mutanenta su yi haka.

Bayan sun An gama ganawa: Bilqis ta ga aqidar mutanenta ta sauya a gaban Sulaiman. Sai ta gane cewa rana da mutanenta suke bautawa ba komai bace face daya daga cikin halittun Allah.

A Ranar Hasken imani ya lullube cikin zuciyarta da haskawa da hasken da ba ya gushewa, shi ne hasken Musulunci.

Bilkis ta gane ashe masarautar Sulaiman ba kamar fadar da ta taba gani ba. Ta shaida hikimarsa da kaskantar da kai tare da karfin ikonsa kuma ta yarda da shi a matsayin manzon Allah. Ta tuba ta musulunta tare da al’ummarta.

Tarihin ziyarar sarauniya Bilkisu zuwa gurin Annabi Sulaiman, tarihi ne da karshen sa ya zamo mai ban kaye sosai, inda a karshe sarauniya Bilkisu ta ayyana da kanta cewa:

” YA UBANGIJI NA LALLAI NA TAFKA KUSKURE (A BAYA) YANZU NA MIKA WUYA GA ALLAH UBANGIJIN KOWA-DA-KOMAI, TA HANYAR ANNABI SULAIMAN”.

Kur’ani sura ta 27 aya ta 44.

A Wata Ruwayar Ance Ta Aure Ta.

WAFATIN ANNABI SULAIMAN

Annabi Sulaiman ya rayu kuma ya yi mulki cikin daukaka. Yawancin aikinsa na jama’a aljanu ne suka yi shi a matsayin hukunci don sanya mutane gaskata cewa aljanu basu da ilimin gaibi. Sulaiman ya koya wa mutanensa cewa Allah ne kadai ya san irin wannan ilimin. Hatta wafatin Annabi Sulaiman ya zama darasi akan haka.

Aljanu ko annabawa ba su san makomar gaba ba, sai ga Allah shi kadai.

Sulaiman yana zaune rike da sandar sa, yayin da yake kula da wasu aljanu da ke aiki a cikin mahakar ma’adinai. Aljannun da suke tsoron Annabi sulaiman, sun mayar da hankali sosai kan ginin a lokacin da Allah ya yi niyyar dauke Ran Annabi Sulaiman.

Ba wanda ya san mutuwarsa, sai bayan kwanaki, wata tururuwa mai yunwa ta fara lallasar sandarsa ta katako. Tana cikin ci sai sandar ta karye, gawar Annabi Sulaiman da ke jingine a kanta ta fadi kasa.

Mutane suka ruga wurin Annabinsu, nan da nan suka gane cewa ya rasu tun da dadewa. Don haka kowa ya gane cewa da aljanu sun mallaki ilimin gaibi, da ba za su azabtar da kansu suna aiki tukuru ba, suna tunanin Sulaiman yana kallonsu.

Rayuwa da mutuwar Sulaiman Lallai suna cike da abubuwan al’ajabi waɗanda ɗan adam zai iya samun darussa masu ban mamaki daga gare su.

“Kuma a lokacin da Muka wajabta wa Sulaiman mutuwa, babu abin da ya nuna wa aljani mutuwarsa face wata kwaro daga kasa tana cin sandarsa. To, a lõkacin da ya faɗi, ya bayyana ga aljannu cẽwa lalle ne dã sun san gaibi, dã ba su zauna a cikin azãba mai wulãkantãwa ba. ( 34:14 )

Ya Rasu A Shekara ta 931 Kafin Haihuwar Annabi Isa (AS) Yana Da Shekaru 53 A Duniya.

Madogarar Wannan Rubutu

Story of Prophet Sulaiman/Solomon (pbuh)
Na Ibn Kathir

Don Neman Karin Bayani duba

Contact IslamAwareness@gmail.com for further information

See also  Tarihin Annabi Sulaiman/Suleman (AS) Kashi Na (2)

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button