Jamb

Abubuwan Da Yakamata Kasani Gameda Jamb Regularization

Lokacin Da kaje/Kika Je, JAMB CBT CENTER Aka ambaci Regularzation Sai kuji Wani sabon Al’amarin Da Baku sanshi ba, Kokuma Baku Da Cikakken Bayani Akan sa.

–JAMB REGURLARIZATION; tsari ne Na samar Da Admission Ga Wanda Hukumar, JAMB Bata basu Admission ba, a Lokacin Dasuka samu Admission Na Makarantar Su(Banda Na JAMB)

Eh Admission Na Makarantar su, Misali Jami’a, Kokuma NCE Ko Diploma.



MEYASA HAKAN?


•Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Makarantun Gaba Da Sikandire (JAMB) a Dokar ilimi ta Kasa itace take Da Hurumin tantancewar Farko Sannan ta Baka admission Kafin Makarantar ka.

a Farko-Farkon Lamari Dalibai Sun kwana Da tsammanin Cewar Jami’a Ce Kadai Ake Shiga da JAMB kafin daga Bisani, suka Fara Sanin Mafi Yawa Daga Cikin Makarantun gaba da Sikandire, Baza su baka admission ba, Sai KAYI JAMB.

Wannan Dokar Hukumar JAMB takara karfa fa ta Ne a ‘Yan Shekarun Nan.

Wannan Shine Dalilin Da Makarantun gaba da Sikandire Dayawa Suka Soke Tsarin Pre-ND a Diploma Dakuma pre-nce, a NCE, Sakamakon ko daka Kayi daya daga Cikin Su, Har Ila yau Ana Buqatar Ka sake Rubuta Jarrabawar JAMB kafin Makarantar ta baka Admission, Bayan hukumar JAMB ta baka.

Kamar yanda Nafadi a Yanzu Hukumar JAMB tana Cigaba da kalacin Dukkannin Sauran Makarantun gaba da Sikandire, Kan Suma subi wannan tsarin Na Cewar Makaranta bazata fara bada admission ba, har sai Dalibi yafara samun Admission DAGA JAMB.

a Karon Farko Dokar Tafi Tsanani ne Akan NCE, Polytechnic Dakuma Jami’o’i, Amma daga Bisani Hukumar JAMB ta shigar Da tsarin Zuwa Wasu Makarantun Monotechnics, Ma’ana kebantattun Makarantu a wani Bangare Guda Daya, kamar irin su kwalejin Aikin Noma(College of agriculture) Da kwalejin koyon Aikin shari’a(Legal)
a Yanzu Za’a Iya cewa tsarin JAMB kafin Admission, ya Kara de kowanne Bangare Da sashi Na Makarantun gaba da Sikandire, a Fadin Nigeria, in Banda school of Nursing, Kokuma College Of health Da wasu Yan Kadan.


See also  Abubuwan Da Yamata Ku Yi, Bayan Rijistar JAMB

—Menene Amfanin JAMB REGURLARIZATION?


Amfanin Sa ya kasu Bangare Biyu Ga Wanda Yayi diploma da Wanda Yayi Jami’a.

Wanda Yayi Diploma; Dalibin da yayi Diploma, Ko NCE Wanda a Lokacin Hukumar JAMB Bata Bashi Admission ba, Kokuma Ma beyi jamb din ba a shekarar, to a Lokacin Dayake, bukatar Shiga Jami’a, ta Hanyar Direct Entry, Dole sai yayi REGURLARIZATION, domin Hukumar JAMB tafara Bashi JAMB Number.

Dalibin Da Yayi Jami’a; Zai Yuwu Ace Dalibi ya kammala Jami’a batare da Hukumar JAMB ta Bashi Admission ba, Sai de Dalibi Bazai samu halartar Yiwa kasa Hidima ba(NYSC) Har sai Yayi JAMB REGURLARIZATION.

Hukumar JAMB itace take Amincewa da Cewar ka, kammala Jami’a Kuma zaka iya yin Hidimar kasa ko A’a.

JAMB REGURLARIZATION a takaice; Yana Nufin wani tsari ne Na Hukumar JAMB, da takeso dole tasan Dukkan Daliban Dasuke karatu a Makarantun gaba da Sikandire, domin ta a Dana Bayanan Su (Matriculation List)
a Wannan Shekarar hukumar JAMB ta Kara Gargadin Makarantu da Kada Su Kara Bawa, Wani Dalibi Admission ba tare Da hukumar tafara Bashi ba.

Kusani Dalibai babu wani Admission, halatacce inde Sunan ka, baya cikin Matriculation List Na JAMB.

Mai karatu Zai Ce to Yaya batun Masu Part time fa, Kokuma karatu daga gida (Distance learning)

Sai Nabaka Amsar Cewa dukan su hukumar JAMB ce take fara basu Admission, domin akwai Nasu tsarin Na Daban, Wanda ya hada hadda Daliban Dasukayi Jami’a a Wasu kasashen(ABROAD STUDY) Dakuma Masu Part Time ko affiliate program.


NB: Dalibai Musani Cewa JAMB REGURLARIZATION Bashi bane Change of Admission Letter.

Zaku Iya fada Mana Wasu abubuwan Dasuka Shige Muku Duhu, Domin Yin Bayani Akai.

See also  Cikakken Tarihin hukumar Jamb

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button