University
Cikakken Bayani Gameda Intra Department Transfer (IDT)
• Me ake nufi da Intra Department Transfer ?
• Yaya ake yin Transfer din ?
• Kowace Jami’a tana yi ?
• Menene Requirements din ?
• Me ake nufi da Intra Department Transfer ?
Shima Kamar Inter Faculty Transfer ne, akan yishi ne a duk lokacin da dalibi ya zama baya gane karatu a wannan department (idan ya zama baya cin Mafi yawan kwasa-kwasan da akeyi a department din) ko kuma sakamakon wani karbabben dalili.
• Yaya ake yin Transfer din ?
Hanya Mafi sauki itane kawai kaje ka samu Level Coordinator dinka kayi masa bayani, shi zai Dora ka a hanyar yadda akeyi.
• Kowace Jami’a tana yi ?
Ehh, kowace Jami’a tana yi, kuma kowanne Department yana karba.
• Menene Requirements din ?
1• Dole ya zama kana da CGPA 1.00 mafi karanci
2• Sannan ya zama kana aji biyu ne (200 level)
3• Idan kuma dalibi bai tashi yin Transfer din ba saida ya kai aji uku (300 level) to idan har yayi nasarar yin Transfer din to sai ya maimaita Level 300 din a sabon department dinda ya koma, Sakamakon dokar Jami’o’i tace ana bukatar dalibi akalla ya share Shekara uku yana karatu a department kafin yayi graduation daga wannan department din.
4• Dole sai an samu amincewa tsakanin Departments din guda biyu (Inda zaka bari da inda zaka je) sannan Dean yayi endorsing.
5• Duka Maki dinda dalibi ya samu a tsohon program din to za’ayi transfer dinshi zuwa sabon Department dinda ya koma.
6• Sannan Sau daya akeyin Transfer din.