NYSC

NYSC : Cikakken Bayani Gameda Banbancin Remobilization da kuma Revalidation

National Youth Service Corps (NYSC)



• Remobilisation ba na kowa da kowa bane



•Bambancin REMOBILIZATION da kuma REVALIDATION





•Remobilisation ba na Kowa da Kowa bane



Hukumar gudanarwa ta dalibai masu yima kasa hidima (Bautar Kasa) ta fitar da Sanarwa akan Remobilisation inda take bada sanarwar cewa idan lokacin da ta bada da farko ya cika ba zata kara wani ba.

Saidai miliyoyin tambayar da dalibai sukeyi shine kowa ne zaiyi Remobilisation din ? A’a ba kowa bane sai wanda yake a Batch B (NYSC 2020 BATCH B).


•Me ake nufi da Remobilisation ?




A karkashin wannan rubutun zaka fahimci abinda ake nufi da REMOBILISATION kai har ma da REVALIDATION.



REMOBILISATION wani terms ne na masu yiwa kasa hidima da suke amfani dashi.



REMOBILISATION wani tsari ne da yake bawa dalibin da zaiyi wa kasa hidima damar sabunta Program dinsa na yiwa kasa hidimar, sannan ya Cigaba daga inda ya tsaya.


•To Su waye suke da damar yin REMOBILISATION din ?




Wadanda suke da damar yin REMOBILISATION sune wadanda sukayi Online registration na tafiya Bautar kasa din, lokacin da aka fara, kuma har sun tafi Camp sun fara komai da komai amma daga baya sai wani matsala ya hanasu Cigaba da zama a Camp din.

To wadannan sune wadanda zasuyi applying (nema) REMOBILISATION aduk lokacin da hukumar ta bada damar hakan domin suje su karasa program din nasu.



•Misali:



Mr. A ne yayi Online registration na NYSC yabi duk wasu Process har ya zama an tura shi Camp, bayan ya fara da kamar Sati daya sai wani dalili (Kamar rashin lafiya) ya hana shi karasa zaman Camp din, dan haka ya koma gida, to yanzu yaji sauki dan haka zai koma ya karasa Camp din nashi, to sai yayi REMOBILISATION.


See also  NYSC : Cikakken Bayani Gameda Monthly Clearance Status

•Me ake nufi da REVALIDATION ?




REVALIDATION shima kamar REMOBILISATION ne ta bangaren wanda zaiyi shi, domin ba fresh Candidate bane yake yi, a’a wanda daman ya Riga yayi ne.



REVALIDATION wani tsari ko hanya ne da yake bawa dalibin da zai yiwa kasa hidima damar Sabunta Online Registration na NYSC din sa da daman ya Riga yayi.



•Wane Coper ne yake da damar yin REVALIDATION ?

Gungun daliban da suke da wannan damar sune: wadanda daman sun riga sunyi registration din su na NYSC lafiya lau, amma sai suka ki zuwa suyi reporting a Orientation Camp saboda wasu dalilai ko kuma haka kawai ba tare da wani dalili ba, to wadannan sune zasu yi REVALIDATION.



Misali:

Mr. B ne yayi Online registration na NYSC din sa, sai aka tura shi Bayelsa acan zaiyi Camp to amma sai yaki zuwa yayi reporting a Bayelsa din har lokacin ya wuce ko da karbabben dalili ko ba dashi ba, to anan ana bukatar Mr. B yaje yayi REVALIDATION.



Saidai fa Shi REVALIDATION ba kamar REMOBILISATION bane, shi REVALIDATION ana yin sa ne by Batch amma ba by Stream ba.

Idan kayi missing bakayi reporting zuwa Camp din ba a wannan Stream din a wannan Batch din, to ba zaka iya yin Revalidation din ba a wani stream, sai dai kuma ka jira wani Batch din.

Amma kar ka damu, domin kuwa idan har Corp member bai tafi Camp din ba a Stream din da ya kamata ya tafi ba, to kai tsaye an cire shi daga wannan Stream din an kaishi na gaba, dan haka babu maganar REVALIDATION kenan, Amma idan ya zama wannan Stream din shine na karshe a wannan Batch din to ba za’a daukeshi kai tsaye akaishi a wani Batch ba dole sai yayi Revalidation.



Misali:

Mr. C ne zai tafi Service a Stream i, to amma sai bai tafi ba, to anan ba zaiyi REVALIDATION ba, kai tsaye (Automatically) an mayar dashi Stream ii.

Amma idan Mr. D zai tafi Service a Stream ii sai bai tafi ba, kuma Stream ii dinnan shine karshe a wannan Batch din, daga wannan sai wani Batch kuma, to anan dole sai Mr. D yaje yayi REVALIDATION.



Bissalam

ASOF_2021

12/02/2021

Arewastf@gmail.com

See also  NYSC : Cikakken Bayani Gameda Monthly Clearance Status

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button