KARATUN MAGANI (PHARMACY) A NIGERIA
Da farko yakamata musan cewa karantar ilimin sanin magunguna(pharmacy) bawai yatsaya a sanin sunan su bane kawai. Wannan ilimin yahada da sanin yadda ake hada magungunan a masana’antu,kayan da ake hada magungunan,yadda suke aiki a jikin mutum,da sauransu.
Karatun pharmacy a Najeriya yana daukan kimanin shekaru biyar 5 ga wanda sukai jarabawar UTME suka fara daga aji daya kenan 100L, ya kandau kimanin shekaru hudu 4 ga wadanda suka shiga jami’a ta D.E waro suka fara da aji biyu 200L. Wanda ya kammala wannan karatu,ana rubutawa a shedar kammala karatunsa (certificate) cewa ya kammala #B_Pharm wato ilimi a sanin magunguna. Ana kiran wanda yakammala wannan karatu da pharmacist
Saidai yanzu wasu makarantu sun qara tsawaita zangon wannan karatun. Dalibi zai kai kimanin shekaru shida 6 kafin yakammala kenan ga wanda suka fara daga aji daya100L ko kimanin shekaru biyar 5 ga wanda suka fara daga aji biyu 200L. Ana kiran wannan mai dogon zango da Pharm.D. Pharm.D yafi bada kulawa ta fannin (clinical base) fiye da B.pharm. makarantu kamar jami’ar Bayero suna bada shedar Pharm.D ne jami’ar Ahmadu Bello kuwa suna bada shedar B.pharm ne. Saidai nan da wani lokaci kusan mafiya yawancin jami’o’in zasu koma bada pharm.D.
Wani abin mamaki shine,wannan tsangayar ta pharmacy ta rabu kusan kashi biyar zuwa shida (departments). Atakaice,idan ka kammala wannan karatu,kamar ka kammala abubuwa shida ne a fanni daban daban, wanda ya hada da ;
•Clinical pharmacy
•Pharmacognosy and Drug development
•Pharmaceutical and medicinal chemistry
•Pharmaceutics and industrial pharmacy
•Pharmacology and toxicology
•Pharmaceutical microbiology and biotechnology
Abinda ake bukata wajen bada gurbin karatu (Admission)
1. Credit biyar 5 a jarabawar kammala sakandiri waec, neco ko Gce. A darussan English, Mathematics, Biology, Chemistry, Physics.
Ga masu shigan ta D.E 200L
1. Sakamakon jarabawaru IJMB mai kyau akalla a darussa uku Physics, Chemistry,da Zoology ko Biology.
Akwai makarantu masu karbar sakamakon digiri a bangaren tsangayar sciences.ko HND a medical laboratory science ko biotechnology da akalla upper credit.
Ana samun sakamako B.pharm ko pharm.D a jami’o’i ne kadai a Najeriya. Masu zuwa makarantun koyon aikin lafiya(school of health science and technology) basayin pharmacy. Saidai wasu nayin *Pharmacy technology* wannan ba matakin su daya da pharmacy ba. Kuma wanda yakaranci wannan ba pharmacist bane, technologist ne.
Wasu makarantu sukan bada sharadin cewa duk dalibin daya gaza kai 2.40 CGPA a bisa 5.00 a kowane aji toh bazaije ajin gaba ba.idan kuma ya gaza kai hakan sama da sau biyu zuwa uku to za’a janye shi daga karatun pharmacy gaba daya.
Kasancewar wannan karaatu akwai gasa sosai wajen nemansa,akwai bukatar dalibi yasamu maki sosai a jarabawar Jamb don samin gurbin wannan karatu.
Darussan da ake gabatarwa a kowane aji
✓100L
Biology
Chemistry
Physics
Mathematics
General studies
Kowanane yakan rabu kashi uku ko sama da haka a kowace semester
✓200L
Biochemistry
Anatomy
Histology
Physiology
Cardiovascular system
Gastrointestinal tract& Biliary
Homeostasis and urine
Introduction to pharmaceutics
Introduction to pharmacognosy
Fundamental pharmaceutical microbiology
Introduction to industrial pharmacy
General studies
✓300L
Pharmaceutics
Pharmaceutical chemistry
Pharmacognosy
Pharmacology
Pathology
Industrial pharmacy
pharmaceutical microbiology
Biotechnology
✓400L
Industrial pharmacy
Sterile pharmaceutical product
Pharmaceutical chemistry
Pharmacology
Clinical pharmacokinetics
Pharmacy management &Entrepreneurship
Cosmetic science and drug delivery
Biopharmaceutical
Pharmaceutical microbiology
Introduction to clinical pharmacy
Immunology &blood products
Phytoevaluation & phytoanalysis
Ethics and jurisprudence
✓500L
Industrial pharmacy & validation
Principles of biotechnology and fermentation
Pharmacology
Herbal& alternative medicine
Veterinary pharmacy
Pharmacotherapeutics
Pharmacy practice and communication skills
Clinical clerkship
Seminar/project
Wannan shine yadda ake gudanar da karatun Pharmacy a takaice.
Musani cewa tsarin wasu makarantu ya banbanta dana wasu.
Bayan kammala wannan karatun, dalibai sukan tafi wurin sanin makamar aiki(internship).shima wanan yana daukar shekara daya kafin tafiya hidimtawa kasa(NYSC).
????️
UMAR LAWAL,
National program coordinator.
ASOF 2023
WhatsApp
08086251045