Tarihin Annabi Sulaiman

Tarihin Annabi Sulaiman/Suleman (AS) Kashi Na (2)


Wata rana Suleman ya tara rundunarsa, ta bataliyoyin mutane, da aljanu, da tsuntsaye, da dabbobi daban-daban. Zai kai su ƙasar Askalon.

Suna wucewa ta cikin wani kwari, sai tururuwa ta ga rundunar da ke gabatowa, sai ta yi magana don ta gargaɗi sauran tururuwai: “Ku gudu zuwa gidajenku! Ga Annabi Sulaiman Nan Da Rundunar sa. Annabi Suleman da jin wannan magana ta tururuwa sai ya yi murmushi. Ya yi murna da tururuwa ta san shi Annabi ne da ba zai cutar da halittun Allah da gangan ba. Ya godewa Allah da ya tseratar da rayukan tururuwai.

Allah Ta’ala ya ce: “ Kuma aka taru a gaban Sulaiman da rundunoninsa na aljannu da mutane da tsuntsaye, sai aka jera su gaba daya. Har a lõkacin da suka je wa wani rami na tururuwa, wata tururuwa ta ce: “Yã kũ tururuwai! Ku gudu Ku shiga rami ga Annabi Sulaiman Nan Da Rundunar sa Kada Ya Tattake Ku.

Sai (Sulaimãnu) ya yi murmushi, yanã mai jin ni’ima da maganarta, kuma ya ce: “Ya Ubangiji! ayyuka na kwarai da za su faranta maka, kuma ka shigar da ni da rahamarKa a cikin bayinka salihai”. (Karanta 27:17-19 Alqur’ani).

A Urushalima, (Kudus) a kan wani katon dutse, Sulemanu ya gina wajen ibada mai kyau don ya jawo mutane su bauta wa Allah. A yau ana kiran wannan ginin da sunan “The Dome of the Rock.” Daga nan ne kuma wasu gungun mabiya da yawa suka bi sahun Sulaiman wajen gudanar da aikin hajji a Masallacin Harami na Makkah.

Bayan sun kammala aikin hajji ne suka tafi kasar Yaman suka isa birnin San’a. Birnin ya burge Annabi Sulemanu ta bangaren Dabarar su ta yadda suka bi da hanyar ruwa a dukan garuruwansu. Ya yi sha’awar gina irin wannan tsarin hanyar ruwan a kasarsa amma bai da isassun magudanan ruwa.

Sai Ya tashi ya ce a nemo Masa tsuntsun hoopoe (Al Hudahuda) wanda zai iya gano ruwa a karkashin kasa. Ya aika da sigina a ko’ina cikin Jama’ar sa don a kira shi, amma ba a ganshi ba. A fusace ya bayyana cewa in dai tsuntsun bashi da wani kwakkwaran dalili na rashin zuwansa, zai hukunta shi Hukunci mai tsanani.

Daga karshe dai Al Huda-huda ya zo wurin Annabi Suleman (AS) ya na Mai Dukar da kasan kasa cikin Girmamawa, Yana Mai Fadin dalilin jinkirin sa Yace “Na gano wani abu da ba ku sani ba, na je Birnin Sheba (Sab’a) na dawo Muku da Wani muhimman labari.

Annabi Sulemanu ya ce yana son ya sani, kuma ya huce fushinsa. Tsuntsun ya ci gaba da cewa: A “Sab’a Akwai wata Katafariyar sarauniya mai suna Bilkis (Bilqis) da ke mulkinta, wadda ke da Arziki Mai yawan Gaske, ciki har da wani katon Gadon Zinare mai kyau, amma duk da wannan dukiya, Shaidan ya shiga zuciyarta da zukatan mutanenta. Ita ce take tafiyar da tunaninsu gaba daya, na yi mamaki da na ga suna bautar rana ba Allah Ta’ala ba”.

Don Annabi Sulaiman Ya Gaskata da Wannan zance sai Sulemanu ya aiki Al Huda-huda da wasiƙa zuwa ga sarauniya Ya umurci tsuntsun da ya kasance a boye kuma ya lura da komai.

Al Huda-huda yana Tashi Fir Sai Birnin Sab’a, Sai Fadar Bilkisu, Yana Shiga sai ya ajiye wasikar a gaban sarauniya ya tashi ya buya. Cike da zumudi ta bude ta karanta: “Lalle daga Sulaiman yake, kuma hakika! Yana cewa: “Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin kai; muminai na gaskiya sune waɗanda suka miƙa wuya.” (Ch 27: 30-31 Quran).

Sarauniyar ta Shiga Cikin damuwa sosai, ta yi sauri ta kira masu ba ta shawara. Don su mai da martani game da Wannan ƙalubale, domin su ji cewa akwai wanda yake ƙalubalantarsu, kuma yana nuna musu zai yaƙe su sha kaye, Amma ya roƙe su, su yi biyayya ga sharadinsa.

Sai suka gaya mata cewa shawara kawai zasu bata amma hakkinta ne ta ba da umarni a dauki mataki. Tace kuna so ku fuskanci barazanar mamayar Sulemanu da yaƙi? Don haka ta gaya musu: “Sulhu da abota sun fi kyau kuma sun fi hikima; yaƙi kawai yakan jawo wulakanci, yana bautar da mutane, yana lalata nagarta. kyauta da Sulhu kuwa zata sa ta sami damar Gano ko waye Sulaiman da jarumtakarsa, idan Annabi zata fahimta idan kuma mai neman mulki ne zata gane.

Shi Kenan Sarauniya Bilkis ta Shirya mutanen ta da Kayan Dukiyoyi masu tarin yawa ta Aikasu zuwa Wajen Annabi Sulaiman, domin su kai masa A matsayin Gaisuwa domin ta jarraba cewa Annabi Ne Ko Mai Neman Mulki da Dukiya ne.

Tawagar Annabi Suleman sun je sun leko Asirin labarin zuwan manzannin Bilkis da kyautar da Aka Aiko da ita kuma sun gayawa Annabi Sulaiman, Nan take ya ba da umarnin tara Rundunar Mayaka da Tarin Dukiyoyi Kafin Wakilan Bilkisu su kammala isowa. Da wakilan suka iso suka ga tarin Runduna da da dukiyoyi, sai suka gane cewa dukiyoyinsu ba komai ba ne kwatankwacin na daular fadar Suleman, wanda aka yi da itacen sandal da zinariya.

Sun lura Sulemanu ya leƙo asirin zuwansu sai suka yi mamakin yawan sojoji iri-iri, da suka gani, waɗanda suka haɗa da zakuna, damisa, da tsuntsaye. Sai manzannin suka tsaya cak a cikin mamaki, sun gane cewa suna gaban wata runduna ce da ba za ta iya tunkara ba.

Wakilan sun yi mamakin irin Kayan ƙawan da ke kewaye da su. Suna ɗokin ba da kyauta da sarauniyarsu ta Aikosu da ita kuma suka gaya wa Sulemanu cewa sarauniyar tana so ya karɓe su a matsayin Sulhu. Abin da ya yi ya ba su mamaki: ko da yake bai nemi buɗe kyautar ba! Ya ce da su: “Allah ya ba ni dukiya mai yawa, da mulki mai girma, da Annabci. Don haka ni na wuce karbar cin hanci, kawai burina shi ne in yada imani da Tauhidi, da kadaita Allah.”

Ya kuma umarce su da su mayar wa sarauniyar kyaututtukan kuma su gaya mata cewa idan ba ta daina irin ibadar da take yi ba zai tumbuke mulkinta ya kori al’ummarta daga kasar.

Wakilan sarauniya sun dawo da kyaututtukan suka isar da sakon. Sun kuma gaya mata abubuwan ban mamaki da suka gani. Maimakon ta yi fushi, ta yanke shawarar ziyartar Annabi Sulemanu da kanta. Sarauniya Bilkis Ta bar Sheba tare da fādawanta da barorinta, ta aiki manzo ya faɗa wa Sulemanu tana kan hanyarta ya tarye ta.

Annabi Suleman ya tambayi aljanu da ke masa aiki ko wani a cikinsu zai iya kawo masa Gadon mulki kafin ta iso. Sai Wani Aljani Daya daga cikinsu ya ce; “Zan kawo mika kafin a gama zaman nan.”

Annabi Sulemanu bai mayar da martani ga wannan tayin nasa ba; ya bayyana cewa yana son Akawo masa shi cikin sauri. Aljanu sun yi ta gwabzawa Gasa da juna don faranta masa rai, wannan yace zai kawo nan da lokaci kaza, wannan Ma Yafada. Can sai wani daga cikinsu mai suna Ifrit Ya mike tsaye ya ce: “Zan kawo muku shi a cikin kiftawar ido!”

Madogara

Tuntuɓi IslamAwareness@gmail.com don ƙarin bayan Bayani ✍️

See also  Tarihin Annabi Sulaiman/Suleman (AS) Kashi Na (3) Kuma Na Karshe

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button