BAMBANCI TSAKANIN ‘BUKATA’ DA ‘SO’
BAMBANCI TSAKANIN ‘BUKATA’ DA ‘SO’
Rayuwa na tafiya ne akan BUKATA da SO, BUKATA da SO sune sanadarin rayuwa wadanda muke rayuwa dasu kuma muke rayuwa a kansu.
A matsayinka na Mutum akwai bukatar ka bambance zakanin Abinda kake Bukata da abinda kake so, iya bambancewa shi ake kira HANKALI.
Idan ka kasa bambance su da tantancewa to zaka iya daukar abinda kake bukata a matsayin abinda kake so, yin hakan na iya kawo maka cikasa a rayuwa.
BUKATA da SO tamkar KWAKWALWA da ZUCIYA ne. BUKATA na fitowa daga KWAKWALWA shi kuma abinda kake SO yana fitowa daga ZUCIYA.
Zuciya ita ce ke sarrafa ayyukan jikin dan adam yayin da kwakwalwa itace ke tantancewa dacewar yin aikin ko a kasan haka. Zuciya na amfani da jini wajen isar da sakonta yayi da ita kwakwalwa take amfani da GABOBIN HANKALI (MISALI: ido, kunne, hanci, baki, harshe, fatar jiki da sauransu). Duk da yake zuciya kan iya yin aiki tare da kwakwalwa amma wani lokacin kowane nayin nasa aikin.
DON HAKA. Abinda kake so zaka fi jinsa a zuciyarka sannan abinda kake bukata zaka fi jinsa a tunanin kwakwalwarka.
Tunda so yana fitowa daga zuciyane ita kuma zuciya bata gani ko ji don haka abinda kake so koda ya zamanto mara kyau, mara amfani ko mai cutarwa ba zaka ji ba kuma ba zaka gani ba ballantana ka gane.
Tunda abinda ka kake bukata yana fitowa daga kwakwalwa ne don haka zai zama mai amfanarwa ne sannan idan ya zama mai cutarwa zaka ji kuma zaka gani sannan zaka gane.
Abinda kake SO zaka bukaci abin na lokaci kadan ne, kuma a kowanne lokaci zai iya chanjawa saboda ita zuciyata na da saurin chanjawa don haka abinda take soma zai iya chanjawa.
Abinda kake Bukata zai yi wuya kaji baka bukatarsa komai dadewa. Saboda ita kwakwalwa tana da wuyar chanja abinda ta aminta da shi.
Abinda ka ke SO tasirinsa yana shafar gangar jiki saboda daga zuciya yake fita. Abinda kake BUKATA yafi shafar rayuwarka saboda daga tunaninka yake fita.
Kafin ka bukaci abu dole sai kaso abin domin sai SO ya shiga zuciya sannan zuciya ta turawa kwakwalwa ta tantance amfaninsa sosai kafin ita kwakwalwar ta Bukaci abin. Shi kuma abinda kake so yana tsayawa ne kawai a zuciyar.
IDAN KANA BUKATAR ABU zaka ga kusan kowama yana bukatar abin ma’ana BUKATA kusan kowa yana da irinta. Amma abinda kake so yana iya burgeka kai kadai ba tare da kaga wanda ke da irin ra’ayin ba.
ABINDA kake BUKATA to ya shafi rayuwarka ne gaba daya, idan baka samu ba zai iya kawo maka cikas idan kuma ka samu zai inganta rayuwarka.
ABINDA kake SO ya shafi jikinka ko rayuwarka ne a takaitaccen lokaci, gaba kila ba zaka so abin ba don haka koda babu abin ba zai kawo maka cikas a rayuwarka ba.
SO+AMFANI=BUKATA.
KWADAYI+SHA’AWA=SO
IDAN KA FAHIMCI BAYANI NA ZAKA GANE:
BUKATA tafi SO amfani kenan Abinda kake bukata yafi dacewa ka martaba fiye da abinda kake so.
Kana son gida mai kyau, amma kana bukatar abinci domin ka rayu. Kana son motar hawa amma kana bukatar kudin zuba MAI ko da yaushe.
KAR KA DAMU DA ABINDA KAKE SO SOSAI, KAFI DAMUWA DA ABINDA KAKE BUKATA.
IDAN KAYI ABINDA KAKE SO, KABAR ABINDA KAKE BUKATA TO TABBAS ZAKA RASA ABINDA KAKE SO KUMA KA RASA ABINDA KAKE BUKATA.
IDAN KAYI ABINDA KAKE BUKATA KABAR ABINDA KAKE SO TO BA ZAKA YI NADAMA BA.