Tambayoyi a Musulunci

SHIN WANDA YA YI SALLAH BABU ALWALA KAFIRI NE ?Tambaya
Assalamu Alaikum dan’uwa kuma malamina ga tambaya naji wata fatawa wacce ba ni da ilimi akanta, wai idan mutun ya yi sallah babu Alwala wai hukuncinsa sai ya sake kalmar shahada ta shiga musulunci, menene ingancin wannan maganar ? Allah ya taimaka Amiin.

Amsa
Wa alaikum Assalam To malam wannan maganar ta shahara a wajan mutane, saidai a wajan malamai yin sallah babu alwala ya kasu kashi biyu :
Idan ya aikata, amma bai halatta hakan ba, ya san ba daidai ba ne, kamar ya aikata saboda kasala, wannan kam bai kafirta ba, saidai ya aikata babban zunubi.
idan ya aikata yana mai halatta hakan, ko kuma saboda izgilanci ga addini, sannan ba jahili ba ne, ba shi kuma da wani ta’awili, tabbas wannan aikin kafirci ne, har ma malamai da yawa sun hakaito ijma’i akan kafircin wanda ya yi hakan, saboda akwai karyata shari’a a ciki, da kuma wulakantata .
Allah ne mafi sani

Duba : Almajmu’u na Nawawi 2\84 da Minhajussunah 5\204.
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA

11/12/2014

See also  MALAM ZAN IYA ADASHI DA WANDA BA MISULMI BA ?

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button