Tambayoyi a Musulunci

ZAN SAKI MATATA SABODA TANA DA CUTAR AIDS?



Tambaya
Assalamu alaikum. Malam matata ta yi rashin lafiya, da aka gwada ta, sai aka ce tana da cutar aids, ni kuma an gwada ni amma an ce bani da ita, Sannan an gwada ragowar matana, suma an samu ba su da ita, gaskiya malam ina so zan sake ta, saboda kar ta shafe mu, amma ina neman shawara ?

Amsa
Wa’alaikum assalamu To dan’uwa cutar aids tana daga cikin cututtuka sababbi, wadanda ba’a tattauna su ba a manyan kundayen musulunci, saidai idan muka duba manufar da ta sa aka shar’anta saki wato tunkude cuta da matsala, daga daya daga cikin ma’aurata ko su duka, za muga ta tabbata a wannan cuta, tun da ilimin likitanci ya tabbatar da cewa cuta ce mai hadari kuma ana daukarta, don haka ya halatta ka sake ta, saboda wannan dalilin tun da malaman Fiqhu sun halatta raba aure saboda cutar kuturta, kamar yadda hakan ya zo a Minahul Jalil Sharhu Muktasarul Khalil: 6\478 Cutar Sida kuma tafi kuturta tsanani.

Sannan ba za’a kalli cutuwar da za ta yi ba, bayan an saketa, domin yana daga cikin ka’idojin Sharia: kau da kai daga tunkude cutar da za ta shafi wani saboda cutar da za ta game, Cigaba da zama da ita zai jawo ka dauki cutar, kuma iyalanka su dauka, wannan yasa ba za’a waiga zuwa damuwarta ba a nan wurin.

Allah ne mafi sani

Amsawa:- Dr. Jamilu Zarewa
30/8/2015.

See also  BABU BAMBANCI TSAKANIN WIWI DA GIYA A HARAMCI

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button