Tambayoyi a Musulunci

IDAN LIKITA YA ZAMA SABABIN MUTUWAR MARA LAFIYA, ZAI YI KAFFARA!



Tambaya
Assalamu alaikum, Malam don Allah ina da tambaya ni nurse ce to ina aiki aka kawo min patient with respiratory distress na daura shi saman oxygen therapy sai still yake min complain yana jin ciwo, ya rasa inda zai sa kan shi ya ji dadi, sai na kira doctor don ya zo yaji complain na ji bai zo ba, sai na ruba ta mashi paracetamol injection da diazapem don ya samu ya yi bacci, ina ba shi injection din sai condition din ya chanza sai ya fara gasping bai dade ba ya ya rasu, na san lokacin shi ne ya yi, amma sai Ni ke tunanin ko injection din da na ba shi ita tasa ciwon ya kara rikecewa, sai na yi browsing a internat sai na ga ashe ba’a yi ma mai respiratory distress diazapem.
Tambaya ta shine zan yi azumin kaffara ne koko tun da ni nayi ne don in taimake shi ban san tana da illa ba ? nagode

Amsa
Wa alaikum assalam,
Za ki yi kaffarar kisan kuskure saboda a Ka’idar likitanci Nurse ba sa bada magani ko Allura sai da iznin likita ko shiryarwarsa, ke kuma kin kuskure kin ba shi maganin da bai kamata ya sha ba kafin likitan ya zo, kamar yadda kika yi bayani, don haka ke ce kika zama sababin mutuwarsa.

Rayukan mutane amana ne, ya wajaba Likitoci su yi taka-tsantsan wajan zama sababin salwantarsu, gushewar dakin Ka’aba ya fi sauki a wajan Allah fiye da kashe Musulmi.
Idan likita ya yi sakaci wajan TIYATA, ko kuma hada magani ko ya kuskure wajan abin da ya kamata, har Mara lafiya ya mutu, zai yi kaffara, saboda kisa ne na kuskure, kisan kuskure kuma ana yi masa kaffara kamar yadda Allah ya yi bayani a aya ta (92) a Suratun Nisa’i.

Za ki yi kaffara ta hanyar biyan diyyar rai da kuma Azumin watanni biyu à Jere.
Allah ne mafi sani

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA

23/01/2020

See also  WALIMAR SAUKAR AL-QUR'ANI!

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button