Ramadan

Falalar Azumin Ramadan Da Wasu Kadan Daga Hukunce-hukuncensa.

Azumin watan Ramadana wajibi ne ga dukkan Musulmi baligi mai lafiya ba mara lafiya ba, wajibcin azumi kamar yadda Allah ya fada acikin Al’kur’ani da fadarsa yana cewa: “Ya ku Muminai Allah Ya wajabta muku yin azumi kamar yadda ya wajabta ma wadanda suka zo kafin ku, ko za ku ji tsoron Ubangijinku.

Kwanaki ne kididdigaggu, wanda ya kasance a cikinku bai da lafiya ko kuma yana kan tafiya, to ya rama abin da ya kubuce masa a wasu ranakun, wadanda kuma ba za su iya yin azumin ba, to su ciyar da Miskinai, amma wanda yake da damar ciyar da miskinai da yawa, to ya yi alkairi ne a wajenshi, lallai yin azumin ya fi alkairi a gare ku, idan kun san wannan alkairin da ke cikin azumin.

Lallai watan Ramadana da aka saukar da Alkur’ani a cikinshi, shiriya ne ga mutane, sannan kuma akwai ayoyi bayyanannu a cikinshi masu shiryarwa zuwa ga Allah da bayyana hukunce-hukunce. Duk wanda ya halarci ganin watan to ya azumce shi, wanda kuma bai da lafiya ko kuma yana kan tafiya, to ya biya abin da ya tsere masa a cikin sauran wasu ranakun, Allah sauki yake nema daga wurinku ba wahalarwa ba, Allah yana son ku cika adadin azumin, sannan yana son ku yi masa kirari daga abin da ya shiryar da ku, ko za ku gode masa?”.

Allah ya saukar da mafificin Littafi (Alkur’ani) a cikin watan Ramadana, a mafificin dare (Lailatul Kadri).

An karba daga Abdullahi bin Abbas, Allah ya yarda da su, yake cewa “Allah Ya saukar da Alkur’ani daga Lauhil Mahfuzi izuwa saman Duniya (a cikin Ramadana aka saukar da Alkur’ani daga Lauhil Mahfuzi zuwa saman Duniya, a dakin Baitul ilimi), Mala’ika Jibril (AS) shi kuma daga nan yake debo ayoyinsa zuwa ga Annabi (SAW), sai da ya shafe shekaru 23 yana kan wannan aikin.

See also  FITAR MAZIYYI GA MAI AZUMI

Hadisai da yawa sun fadi falalar Azumin Ramadan.

Daga cikin Hadisai akwai:

قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: “إِذَا جَاءَ رَمَضَانُ فُتِحَتْ أَبْوَابُ الْجَنَّةِ وَغُلِقَتْ أَبْوَابُ الْنِيرَانِ وَصُفِّدَتِ الشَّيَاطِينَ.” (رواه البخارى)

Ma’ana:

Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Idan watan Azumin Ramadan ya zo, ana bude kofofin Aljanna, kuma ana rufe kofofin wuta, kuma ana daure shaidanu.” (Bukhari ne ya rawaito).

عَنْ أَبِى سَعِيدِ الْخُدْرِى رَضِيَ اللهُ عَنْهُ أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: “مَا مِنْ عَبْدٍ يَصُومُ يَوْمًا فِي سَبِيلِ اللهِ إِلاَّ بَاعَدَ اللهُ بِذَلِكَ عَنِ النَّارِ سَبْعِينَ خَرِيفًا.” (رواه البخارى ومسلم)

Ma’ana:

An karbo daga Abi Sa’idil Khudri (R.A) ya ce, Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Babu wani bawa da zai azumci rana daya saboda Allah face sai Allah ya nisanta fuskarsa ga barin wuta shekara saba’in.” (Bukhari da Muslim ne suka rawaito).

عَنْ أَبِى هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللهُ عَنْهُ أَنَّ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: مَنْ صَامَ رَمَضَانَ إِيمَانًا وَاحْتِسَابًا غُفِرَ لَهُ مَا تَقَدَّمَ مِنْ ذَنبِهِ.” (رواه أحمد)

Ma’ana:

An karbo daga Abu Huraira (R.A) ya ce, Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Duk wanda ya azumci watan Ramadan yana mai imani da neman lada za a gafarta masa abin da ya gabatar daga zunubinsa.” (Ahmad ne ya rawaito).

Hakika, Allah Madaukakin Sarki ya yi alkawari gwaggwaba, sakamako ga wanda ya azumci watan Ramadan.

Sannan Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Duk aikin alherin da dan’adam ya yi Allah yana ninka masa lada goma har zuwa dari bakwai.

Allah (S.W.T) yana cewa, sai dai Azumi, shi nawa ne, ni ake yi wa, kuma ni zan ba da sakamakon yin sa.

See also  JININ BARI BA YA HANA AZUMI

Domin mai Azumi yana da farin ciki guda biyu, farin cikin farko lokacin da zai yi buda baki, na biyu kuma lokacin da zai gamu da Ubangijinsa, hakika, warin bakin mai Azumi ya fi turaren almiski kamshi a wajen Allah.” (Muslim ne ya rawaito).

Azumi ya wajaba kan Musulmi, Da ba bawa ba, baligi mai lafiya, amma ba laifi a dinga koya wa yara yin azumin. Mara lafiya da Matafiyi da mai Haila da mai Jinin biki za su rama azumin da ya kubuce musu. Amma tsoho wanda ba zai iya azumtar azumin ba da fursuna da aka yanke wa hukuncin zaman gidan yari har abada sannan kuma akwai aiki mai wuya da aka dora masa kullum, su wadannan azumi ya fadi a kansu. In suna da hali, su dinga ciyarwa.

Mace mai Juna-biyu da mai Shayarwa, su rama azumin in za su iya ko su ciyar.

An karba daga Anas, ya ce, Annabi SAW ya ce “ku dinga yin Sahur, domin shi yin Sahur akwai albarka a cikinsa.“ ba burgewa ba ce mutum ya dinga cewa ‘ai ni ban yin sahur’ albarka mai yawa ta wuce shi.

An karba daga Sahlu dan Sa’adu Allah ya kara yarda da shi ya ce, Manzon Allah SAW ya ce “Mutane ba za su gushe ba cikin alkairi muddin sun gaggauta yin buda-baki” Ma’anar wannan hadisi, sabida Allah ya fada cikin Alkur’ani “summa atimmus siyama ilallai – sannan ku cika azumi zuwa dare” sai Annabi ya koya mana sunnarshi zuwa dai-dai lokacin da ya dace na buda-bakin (ba cikin dare Allah yake nufi ba), sai Annabi SAW ya bayyana da fadarsa ku gaggauta yin buda baki – da rana ta fadi, an sha ruwa.

See also  (DAUSAYIN RAMADAHAN) FA'IDOJI GOMA DA MAI AZUMI ZAI SAMU

Manzon Allah SAW ya kasance in an sha ruwa yana fara bude baki ne da addu’a inda yake cewa “Allahumma laka sumtu wa ala rizkika afdartu – Ya Allah a gareka nake Azumi kuma cikin arzikinka nake buda-baki” mai azumi cikin hadarar Allah yake don haka a wurin mai arziki mai azumi yake shan ruwa.

????Juma’at Kareem ????
⭐️Ramadan Mubarak ⭐️

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button