BloggingTech

Matakan Da Zakabi Idan Kanason ƙirƙirar Shafin Yanar Gizo (Website)

Yadda ake gina shafin yanar gizo wato (Website), wanda zaka iya gudanar da kasuwancinka kokuma neman kuɗi a wannan shafin kuma har Allah yataimake ka ka cimma buƙatar ka..

Kamar yadda kuka sani akan ƙirƙiri shafukan yanar gizo batareda amfani da Programming Languages ba wanda akafi sani da yaren na’ura akan yi amfani da website irinsu WordPress da sauransu domin ƙirƙirar irin waɗannan websites ɗin, sai dai sunada rauni kasancewar bakada cikakken ikon da zaka saka ma shafin tsaro ko ƙayata shi a yadda kakeso..

Shi kuma Wannan ɓangaren da zanyi maku bayani ɓangare ne da ake amfani da Programming Languages wato yaren na’ura domin ƙirƙirar shafukan yanar gizo ko shafukan sada zumunta, wanda kaima idan ka ƙware zaka iya ƙirƙirar shafi irin na FACEBOOK, farko dai Idan kanason kashiga cikin sahun masu ƙirkirar shafukan yanar gizo wato (Web Development) akwai matakan da zakabi kafin sanin yadda zaka iya zama (Web Developer) matakan kuma sune kamar haka: Sanin Programming Languages kamar:  PHP, JS, HTML, CSS, Perl, Python, Sanin “Database” da ilimin yadda ake tafiyar da ita tareda sani da kuma ilimin languages dinta kamar su: SQL, PDO, Sai kuma ka nemi Ilimin networking da sanin yadda yake aiki da shige da fice a yanar gizo, Sannan kuma sai Sanin yadda zaka kare shafin yanar gizo daga masu kutse, Sai kuma Ilimin yadda zaka iya warware duk wata matsala da kan iya tasowa a shafin yanar gizon naka..

Wadannan sune matakan da yakamata kasani idan har kanason gina website kokuma kanason zama (Web developer).

HTML, CSS duk da yanzu Bootstrap ta kwace kasuwar CSS sai kuma SQL sai JavaScript da PHP sun isheka hada kowanne kalan website a duniya..

See also  YADDA ZA KUYI CONVERTING NA VOICE ZUWA TEXT.

PHP yana daya daga cikin Scripting language (Severside) Abinda ake nufi da server side shine yaren yana mu’amala tsakanin server da browser, PHP programming language ne wanda ake amfani dashi wajen developing Website, shine (backend) na Creating Website wato ba kamar HTML and CSS da suke (frontend) ba, Ana amfani da yaren PHP wajen gina Backend na Website, wato yaren PHP yanada matukar sauki sannan kuma idan ka iya shi zaiyi wahala ka rasa ayyukan da zaka gudanar sbd la’akari da cewar kaso 80 na website din duniya da yaren PHP aka hada su, PHP bai tsaya nan ba zaka iya hada abubuwa da yawa dashi bawai sai website kadai ba kamar yadda wasu suke tunani..

www.tizag.com zai taimaka maka wajen koyo PHP..

Wasu suna tabbaya cewa Shin Wajen Hada Website Ana Kashe Kudi..?

wato “Domain Name” na website shine adireshin website. Misali idan ka sayi shago a kasuwa sai mai shagon ya baka unique number da ba kowa bane ya santa kuma dai zatayi wahalar riƙewa dan haka ya kamata ka sanyawa shagonka suna(domain name) ta yadda mutane zasu rinƙa ziyarta kai tsaye batare da sai sun tambaya ba, “Domain name” shine sunan website naka da zakayi register a registrar ta duniya, idan kayi register Domain to zai shiga registrar ta duniya wato “Domain Name System (DNS) yana zuwa da extention .com, .net, .biz… abubuwa kamar haka dai, Kuma sannan tabbas  ana biyan .com 4k ne, .com.ng 1k kaga kenan ya tashi 5k.

Allah Ubangiji Yataimaka.. 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button