Addu'o'i

Karanta addu’ar sujjada na sallah

Wannan addu’a ce da ake karanta ta yayin da kayi sujjadah a cikin Sallah sai kace:

سُبْحَانَ رَبِّيَ الأَعْلَى . (ثلاثَ مَرَّاتٍ)
Subhana rabbiyal-a’la. (3)

Tsarki ya tabbata ga Ubangijina mafi daukaka.


سُبْحَانَكَ اَللَّهُمَّ رَبَّنَا وَبِحَمْدِكَ، اَللَّهُمَّ اغْفِرْلِي.
Subhanakal-lahumma rabbana wabihamdik, allahummagh- fir lee.

Tsarki ya tabbata gare Ka, Ya Allah! Ya Ubangijinmu! Tare da godiya gare Ka. Ya Allah! Ka gafarta mini.


سُبُّوحٌ قُدُّوس، رَبُّ الملائِكَةِ وَالرُّوحُ .
Subbohoon kuddos, rabbul-mala-ikati warrooh.

(Ubangiji) abin tsarkakewa, mai kubuta daga dukkan abin da bai kamace shi ba, Ubangijin Mala’iku da Jibrilu.


اَللَّهُمَّ لَكَ سَجَدْتُ وَبِكَ آمَنْتُ، وَلَكَ أَسْلَمْتُ، سَجَدَ وَجْهِي ِللَّذِي خَلَقَـهُ وَصَوَّرَهُ وَشَقَّ سَمْعَهُ وَبَصَرَهُ، تَبَارَكَ اللهُ أَحْسَـنُ الْخَالِقِين.
Allahumma laka sajadt, wabika amant, walaka aslamt, sajada wajhee lillathee khalaqahu wasawwarahu washaqqa sam’ahu wabasarahu, tabarakal-lahu ahsanul-khaliqeen.


Ya Allah! Gare ka na yi sujada, kuma da Kai na yi imani, kuma gare Ka na mika wuya. Fuskata ta yi sujada ga wanda ya halicce ta, kuma ya yi mata surarta, kuma ya tsaga ji da gani a gare ta. Allah mafi gwanintar masu halitta, ya girma, kuma alherinsa ya yawaita.


سُبْحَانَ ذِي الْجَبَرُوتِ، وَالْمَلَكُوتِ، وَالْكِبْرِيَاءُ، وَالْعَظَمَة.
Subhana thil-jabaroot, walmalakoot, walkibriya’i, wal’azamah.

Tsarki ya tabbata ga (Allah) mai dole, da mulki, da kasaitar daukaka da girma.


اَللّهُمَّ اغْفِرْلِي ذَنْبِي كُلَّهُ، دِقَّهُ وَجِلَّهُ، وَأَوَّلَـهُ وَآخِـرَهُ وَعَلانِيَّتَهُ وَسِرَّه .
Allahummagh-fir lee zanbee kullah, dikkahu wajillah, wa-awwalahu wa-akhirah, wa- ‘alaniyyatahu wa-sirrah.

Ya Allah! Ka gafarta mini zunubaina dukkaninsu, kananansu da manyansu, na farkonsu da na karshensu, bayyanannunsu da boyayyunsu.


اَللَّهُمَّ إِنِّي أَعُوذُ بِرِضَاكَ مِنْ سَخَطِكَ، وَبِمَعَافَاتِكَ مِنْ عُقُوبَتِكَ، وَأَعُوذُ بِكَ مِنْكَ، لاَ أُحْصِي ثَنَاءً عَلَيْكَ، أَنْتَ كَمَا أَثْنَيْتَ عَلَى نَفْسِكَ.
Allahumma innee a’uzu biridaka min sakhatik, wa-bimu’afatika min ‘ukubatik, wa-a’uzu bika mink, la uhsee thana-an ‘alayk, anta kama athnayta ‘ala nafsik.

Ya Allah ina neman tsari da yardarka daga fushinka, da kuma rangwamanka daga ukubarka, kuma ina neman tsari da kai daga gare Ka. Ban isa na tuke ga yabo mai cancanta gare ka ba; kai dai kamar yadda Ka yabi kanKa ne.

See also  Karanta Addu'ar Ranar Arfa

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button