Addu'o'i

Addu’ar Tashi daga Majalisi (Domin Neman Yafewa Ga Abin Da Ya Gudana A Cikin Majalisin)A’isha, Allah ya yarda da ita, ta ce: Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, bai taba zama a wani majalisi ba, ko ya karanta Alkur’ani, ko ya yi wata sallah face ya cika da wadannan kalmomi.
سُبْحَانَكَ اَللَّهُمَّ وَبِحَمْدِكَ، أَشْهَدُ أَنْ لاَ إِلَهَ إِلاَّ أَنْتَ أَسْتَغْفِرُكَ وَأَتُوبُ إِلَيْكَ.
Subhanakal-lahumma wabihamdik, ashhadu an la ilaha illa ant, astaghfiruka wa-atoobu ilayk.

Tsarki ya tabbata a gare Ka, ya Allah, da yabo gare Ka. Ina shaidawa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Kai, ina neman gafararka, kuma ina tuba izuwa gare Ka.

Sai A’isha ta ce: Ya Manzon Allah! Na lura cewa ba ka taba zama a wani majalisi ba, ko ka yi karatun Alkur’ani, ko kayi sallah face ka fadi wannan kalmomi. Sai ya ce; “Kwarai. Duk wanda ya fadi wani alheri sai wadannan kalmomi su zama kamar hatimi ne ga alherin da ya aikata, wanda kuma ya fadi sharri, sai su zama kaffara ne gare shi.

See also  Addu'ar tafiya Zuwa Masallaci

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button