Tambayoyi a Musulunci

ZAN IYA YIN MAGANA LOKACIN PRE-KHUDBA ?



Tambaya

Asalamu Alaikum.
Allah ya karawa Dr Fikira da Fasaha.
Tambaya: idan mutum ya zo masallacin jumaa ya samu ana pre-khudba shi kuma yana so ya karanta Suratul Kahfi, to zai iya karantawa ya jiyar da kansa sautin karatun koda na kusa da shi suna ji?

Amsa
Wa alaikum assalam, zahirin hadisin da ya zo akan hana yin magana lokacin da ake hudubar juma’a bai game har da pre khudba ba, don haka za ka iya yin magana,ko ka karanta alqur’ani a lokacin da ake yinta.
Pre- khudba ta banbanta da huduba, saboda akan yi ta kafin Muktarin Juma’a ya shiga, sannan a lokuta da yawa za ka ga ba liman ne yake yi ba, Hani da umarni a shari’a abu ne da yake hannun Allah da manzonsa, wannan ya sa za’a takaita a inda ya zo a nan.
Hadisi mai lamba ta: 841 a sahihil Bukhari ya tabbatar da cewa : sai liman ya fito zai hau minbari ya fara huduba sannan mala’iku suke nannade takardun su, su zauna su saurari wa’azi da ambaton Allah, wannan sai ya nuna Pre-khudba ba ta daukar hukuncin hudubar juma’a wajan wajabta yin shiru da sauraro.
Allah ne mafi sani.

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA 3/Ramadan 1437

See also  WANDA YA SAUKE AL-QUR'ANI, BAI SAN FASSARAR SHI BA , YA YI LAIFI ?

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button