Tambayoyi a Musulunci

WANDA YA NEMI MATAR DA TAKE IDDA, ZAI IYA AURENTA BAYAN TA KAMMALA!!


*Tambaya*
Assalamu alaikum.malam ina kwana ya aka ji da jama’a, Allah ya kara ma malm lafiya da tsawan rai mai albarka.
Tambayata shiine idan wani ya nimi macen da take idda yace mata yana son ta kasance matar shi nan gaba wai aure ya haramta a gare su in ta gama iddan?

*Amsa*
Wa’alaikum assalam, ya aikata sabon Allah, tun da Ubangiji ya haramta neman auran wacce take idda a cikin suratul Bakara aya ta: (235).

Ya halatta a gare shi ya aure ta bayan ta kammala idda, saboda wancan sabon ba zai haramta masa ita ba.

Idan har aka daura aure a cikin idda, malaman Malikiyya suna wajabta raba auran da kuma haramtata ga wanda ya auretan har abada.

Da fatan kun fahimci bambanci tsakanin neman aure da kuma daura aure a cikin Idda.

Allah shine mafi sani

06/12/2017

Amsawa:✍????
*Dr. Jamilu Yusuf Zarewa.*

DAGA: *ZAUREN ISLAMIC SUNNAH*+2348065575014

See also  MIJINA MAZINACI NE, ZAN IYA JUYA MASABAYA?

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button