WALIMAR SAUKAR AL-QUR’ANI!
Tambaya:
Slm. malam ko akwai nassi da yake nuni akan halarcin yin walimar saukar alqur,ani.??
Amsa
To dan’uwa malamai suna cewa : Yin walimar saukar Alqur’ani ta kasu kashi biyu:
1. Wanda ya sauke Alquir’ani ya yi walima saboda godiya ga Allah, wannan kam ya halatta, saboda nassoshin da suka zo wadanda suke kwadaitarwa akan godewa Allah akan ni’imominsa.
2. Yin walimar saboda riya cewa ibada ce mai zaman kanta, wannan kam bidi’a ne tun da ba’a samu Annabi ﷺ da sahabbansa sun yi ba, don haka yana da kyau wanda ya yi walima ya bayyanawa mutane cewa ya yi ne don godewa Allah, ba wai don kasancewar hakan ibada ce mai zaman kanta ba.
Amma abin da aka rawaito cewa: Umar R.A ya yanka rakumi bayan ya gama haddace & kiyaye suratul-bakara, to wasu malaman hadisin sun raunana shi kamar Ibnu-kathir A Musnadul-farouk 2\571, saboda a cikin sanadinsa akwai Abu-bilal Al-ashhary, wanda Dara-kudni ya raunana.
Allah ne mafi sani
Don neman Karin bayani duba fatawaa Allajna Adda’imah 2\488.
29/1/2015
Dr. Jamilu Zarewa Hafizahullah