Tambayoyi a Musulunci

SANYA HAKORIN MAKKA A MA’AUNIN SHARIA?



Tambaya
Assalamu Alaikum Dr, dafatar ka tashi lafiya Alagafarta malam ina neman karin bayani game da Hauren makka da alhazzai suke sakawa akan cewa shima yana haddasa lum’a a lokacin da mutum ya zo kuskurar baki ruwa ba za su taba ainihin Hauren da Allah ya halicci mutum da shi ba?

Amsa
Wa alaikum assalam, a zahiri sanya Haure bayan aikin hajji ba matsala ba ne ta fuskar Lam’a tun da kurkure baki sunna ne a wajan da yawa daga malamai, wannan yasa rashin shafar ruwan ga hakori daya ba zai yi tasiri ba.

Amma zai iya zama matsala saboda yana iya janyo riya, tun da galibi wanda zai sanya yana yi ne saboda yaje hajji ko dan ace masa Alhaji, hakan ya sa barinsa shi ne ya fi.

Idan ya kasance an yi hauren ne da zinare to haramun ne namiji ya sanya saboda Annabi ﷺ ya ce: (An haramta zinare ga mazajen Al’umata, amma an halatta ga matayansu) kamar yadda Tirmizi ya rawaito kuma ya inganta shi a hadisi mai lamba ta: (1720).

Allah ne mafi sani.

1/11/2017

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa

See also  SHIN WANDA YA YI SALLAH BABU ALWALA KAFIRI NE ?

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button