Karanta addu’ar cin abinci ko shan abin sha
Addu’ar cin abinci ko shan abin-sha (Bismillahi).
Malamai da sauran masana suka ce, idan ka lura da cututtukan da mutane suke kamuwa dasu, zaka ga galibin cututtukan ana kamuwa dasu ne ta abinda ake kaiwa baki, abinci ko abinda ake sha, yin addu’a ko fadin “Bismillahi” tana taimakawa kuma tana jawo tsaro daga cututtuka daga wurin Ubangiji, zaka samu tsaro da kula ta hanyoyi guda hudu:
.
1. Idan akwai Sihiri na tsafi acikin abincin, wanda aka zuba saboda kai ko saboda ke, Allah zai tsare ka, zai baka kariya daga sihirin yayin da kace Bismillahi a lokacin da zaka fara cin abincin.
2. Idan akwai Guba (Poison) acikin abincin, wanda aka zuba aciki saboda a cutar da kai, ko saboda a kashe ka, Allah zai baka kariya da tsaro daga wurin sa, saboda ka nemi taimakon Allah, ka kira sunan sa ta hanyar fadin Bismillahi a farkon abincin.
.
3. Idan akwai cuta aciki, kamar communicable diseases, ko transferable disease, irin su Tyhpoid, TB, Ciwon hanta ko ‘Koda (da sauran su da yawa), wanda ana iya ‘daukan su acikin abinci, ko Cokali, Kofi ko Kwanon cin abinci, Allah zai tsare ka daga cutar da zaka iya dauka ta sanadin wannan abincin dake gaban ka, ko ruwan dake cikin kofin da zaka sha.
4. Fadin Bismillahi yayin da zaka ci abinci zai baka tsaro daga shiga wutar Jahannama, saboda kayi koyi da manzon Allah, wanda yayi koyi da manzon Allah kuma toh yana da tsaro daga wuta.