Addu'o'i

Karanta addu’a yayin kiran Sallah

Addu’a yayin kiran Sallah :
Wanda ya ji kiran sallah zai fadi dukkan abin da ladanin yake fadi, sai dai idan yace;
حَيَّ عَلَى الصَّلاَةِ، حَيَّ عَلَى الْفَلاَحِ.
Hayya Alas Salah, Hayya Alal Falah.
Ku taho ga Sallah, ku taho ga babban rabo.

Maimakon haka sai shi ya ce:
لا حَـوْلَ وَلا قُـوَّةَ إِلاّ بِالله.
La hawla wala kuwwata illa billah.

Babu daraba, babu karfi sai da Allah.

Bayan kuma ladan ɗin ya gama kiran Sallah, sai kace:

وَأَنا أَشْـهَدُ أَنْ لاَ إِلَـهَ إِلاّ اللهُ وَحْـدَهُ لاَ شَـريكَ لَـهُ، وَأَنَّ محَمّـداً عَبْـدُهُ وَرَسُـولُهُ ، رَضِيـتُ بِاللهِ رَبَّاً ، وَبِمُحَمَّـدٍ رَسُـولاً وَبِالإِسْلامِ دِينًا .
Wa-ana ashhadu an la ilaha illal-lahu wahdahu la shareeka lah, wa-anna Muhammadan AAabduhu warasooluh, radeetu billahi rabban wabimuhammadin rasoolan wabil-islami deena.

Ni ina shaidawa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai, babu abokin tarayya a gare Shi. Kuma Allah shi ne Ubangiji, kuma Muhammadu shi ne Manzo, kuma Musulunci shi ne addini.


Bayan ya gama amsa kiran sallar, sai ya yi salati ga Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.

Sannan ya ce:
اللّهُـمَّ رَبَّ هَذِهِ الدّعْـوَةِ التّـامَّةِ وَالصّلاةِ القَـائِمَة آتِ محَـمَّداً الوَسيـلةَ وَالْفَضـيلَة وَابْعَـثْهُ مَقـامًـا مَحْـمُوداً الَّذِي وَعَـدْتَهُ إِنَّـكَ لا تُـخْلِفُ الْمِيـعَادَ.
Allahumma rabba hathihid-da’watit-tammah, wassalatil-ka-imah ati Muhammadan alwaseelata wal-fadeelah, waba’ath-hu makaman mahmoodan allazee wa’adtahu, innaka la tukhliful-mee’ad.

Ya Allah! Ubangijin wannan kira kammalalle, da wannan sallar da za a tsayar da ita. Ka ba wa Muhammadu wasila (matsayin kusanci a cikin Aljanna), da matsayin fifiko, kuma ka tashe mu a matsayi abin godewa, wannan wanda Ka yi masa alkawarinsa. Lallai kai ba ka saba alkawari.


Sannan ya yiwa kansa addu’a tsakanin kiran sallah da tayar da ikama, domin addu’a a wannan lokaci ba a kin karbarta.

See also  Addu'ar Tashi daga Majalisi (Domin Neman Yafewa Ga Abin Da Ya Gudana A Cikin Majalisin)

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button