LawShehu Rahinat Na'Allah

Ko ya Halasta mutum ya mallaki Bindiga don kare kanshi ?

Marubuci: Shehu Rahinat Na’Allah



Bindiga na daga cikin makamai masu matuƙar muni da haɗari a Nigeria dama duniya baki ɗaya, saboda zata iya yin ɓarna mai yawan gaske a cikin ƙanƙanin lokaci, don haka Gwamnatin Nigeria tayi dokar data haramta ma mutane mallakar bindiga, to saidai a wasu lokutan da dama mutane sukan buƙaci bindigar ko dan su kare kansu, lafiyar su da dukiyar su lura da yadda ake ta fama da matsalolin tsaron da suka haɗar da satar mutane, kisan gilla da sauran ayyukan ta’addanci.

To idan kana buƙatar bindigar ya za kayi ?

Na farko dai idan har kana bukatar bindigar dole sai an baka lasisi, kuma a duk fadin Nigeria mutane uku ne kacal suke da damar bada wannan lasisin kamar yadda Sashi na 6 na Firearms Act ya bayyana, gasu kamar haka:

a. Shugaban Ƙasa

b. Inspector General of Police

c. Kwamishinan ƴan Sanda na Jiha (bayan ya samu izinin yin hakan daga gwamna)

Saboda haka, idan kana buƙata abinda za kayi da farko Shine kaje babban ofishin ƴan sanda na jiha ko na ƙasa ka tambayi Department ɗin da suke bada wannan lasisin daganan zasu baka wani Form ka cika, sannan ka biya kudin da ake biya na samun lasisin, idan ka cika dukkan sharuɗan da ake bukata sai ka mayar da Form din (bayan ka cika kenan) daganan za’a baka lasisin siyen bindigar.

Sannan lasisin da aka baka dole zaka riƙa sabunta shi a duk Shekara. A wurin sabunta shi dole zaka tafi da bindigar, da kuma harsasan da aka yarda ka siya domin a duba shin kayi amfani dasu, idan har kayi to dole sai ka bada bayanin yadda kayi amfani dasu, ma’ana sai bayar da dalilin da yasa kayi harbi da bindigar. Don haka, idan an baka lasisin ba wai zuwa za kayi ka yita yin harbi anyhow ba.

To wannan lasisin za’a iya bawa kowa ?

A’a, ba kowa bane doka ta yarda a bashi wannan lasisi ba, akwai mutanen da doka tace haramun ne su mallaki bindiga, waɗannan mutanen sune:

a. Yaron da yake ƙasa da Shekara 17

b. Wanda yake da matsalar ƙwaƙwalwa

c. Wanda yake da matsalar Ido

d. Mutum mai zafin rai

e. Wanda bai wuce shekara biyar da fitowa daga gidan gyaran hali ba, saboda laifin yin faɗa ko kuma raunata wani ko barazanar yima wani rauni.

Waɗannan rukunin mutanen ba za’a basu lasisin mallakar bindiga ba.

To wasu irin bindigogi ne ƴan ƙasa suke da damar Mallaka ?

Don haka idan muka duba Firearms act za muga ya kasa rukunin bindigogi zuwa kashi uku kamar haka:

(a) Haramtattun bindigogi

Waɗannan bindigogi sun ƙunshi:

1. Bindiga Mai jigida

2. Bom, gurnati da sauran Nau’ukan makamai masu fashewa

3. Atilari (Artillery)

4. Bindigar Sojoji da suka haɗar da: AK 47, AA, da dai sauran duk waɗanda linzaminsu yakai tsawon 7.62mm, 9mm, .300 inches da kuma .303 inches

5. Tafida gidanka (Revolvers and Pistols)

6. Da dai duk wasu bindigu da ba’a ambace su a lamba ta 2 da ta 3 ba.

(b) Mallakar kai-da-kai (Wato Personal firearms) su kuma sun haɗar da:

1. Shotguns, Amma banda automatic da kuma semi-automatic shotguns, sai kuma shotguns ɗinda na’ura ce ke iya loda masu harsasai, wato wacce ba zuba mata harsasai akeyi ɗaya-ɗaya ba.

2. Sporting riffles, amma banda waɗanda aka faɗe su a lamba ta huɗu dake ƙarƙashin (a) ɗaya (Wato Haramtattun bindigogi)

3. Air guns, air riffles ko kuma air pistols

4. Humane killers of captive bolt type

(c) Bindigar toka (wato muzzle firearms) sun haɗar da:

1. Dane-guns

2. Flint-lock guns

3. Cap-guns

Amma waɗannan Nau’ukan bindigu guda uku dole ne su kasance irin na ƴan farauta ne, haka ma bullet ɗin.

My authorities:
Sections: 3,5,5,6, Schedule: Part I, II, and III

See also  Macen da ke Jinin Haila PAD Nawa ya kamata tayi amfani dashi kullum ?

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button