Shehu Rahinat Na’Allah

SHEHU RAHINAT NA’ALLAH

Dalilin da yasa na sanya sunan Mahaifiya ta a cikin suna na

Wannan ya faru ne tun lokacin ina sakandare (SS1-SS2), duk da kasancewar ina da yayye da kanne amma a cikin mu ni kadai nayi hakan saboda wasu dalilai da zan bayyana su nan gaba.

Ba wai rashin Mahaifi ne
yasa nayi hakan ko rashin kulawar sa ba, kamar yadda wasu suke cewa ko suke tambaya ta.

Hakika ina da mahaifi mai suna ALH. NA’ALLAH (Yusha’u) a Anguwar Hayin Sakaba cikin garin Sakaba dake jihar Kebbi, Kuma suna tare da Mahaifiya ta yau shekara 40 kenan.

Hakika ya kula da ni a Matsayin sa na Mahaifi kamar yadda ya kula da sauran yayan sa, ya dauki nauyin karatu na daga Matakin Firamare har zuwa Matakin Digiri tare da wasu kwasa kwasai da kuma diploma, ban kuma cire sunan sa ba a jikin suna na kamar yadda yake hakkin sa ne.

Cikakken suna na shine SHEHU RAHINAT NA’ALLAH, na Kara sunan mahaifiya ta ne a tsakiya saboda dalilai guda uku, zan anbatawa me karatu guda biyu, na ukun sai a bakin Yan jarida.

1• Wata rana ina bawa mahaifiya ta labarin wasu Shahararrun Mata Yan gwagwarmaya sai take cewa: Ina ma Ina cikin su sai dai gashi banyi karatun boko ba. Ni kuwa dan na faranta mata, sai na yimata Alkawarin cewa Insha’Allah sunan ta ba zai gushe ba tsakanin Alkaluman Marubuta tarihi, kamar yadda sunan waɗannan matan bai ɓace ba to kema naki ba zai ɓace ba, Don haka Zanyi iya ƙoƙari na wajen ganin na tabbatar da duk lokacin da za’a ambaci suna na to sai an ambaci naki sunan

Ina ta tunanin yadda zan cika mata wannan Alkawarin sai na karanta Tarihin Marigayi Gen. Murtala Ramat Muhammad, hakan ya sa naji cewa na samu wata hanya da zanyi amfani da ita wajen cika mata alkawari na, Kasancewar nima ina da sha’awar yin siyasa, sai na yanke shawarar saka sunan ta a Cikin suna na bisa amincewar Mahaifi na

2• Ni da mahaifiya ta tamkar Aminan juna muke, muna da shaƙuwa mai matuƙar ƙarfi har ma tana sanar dani duk wani sirrin ta – bata boye min komai- haka nima bana ɓoye mata komai dangane dani, akwai wasu sirruka a tsakanin mu da babu wanda ya sansu sai Ni kaɗai, hakan ya kara min kwarin gwiwa wajen kara sunan ta domin na sanya ta farin ciki.

3• Daman kuma Ni mutum ne mai son zuwa da wani abu unfamiliar, (Indai Abun bai saɓa ma addini ba) to don haka wannan ma yana daga cikin dalilai na na saka sunan ta

Kuma har zuwa yanzu bana jin zan hana ‘ya’ya na raɓa sunan mahaifiyar su tare da nasu in suna da sha’awar yin hakan.

Bissalam
Shehu Rahinat Na’Allah
Dalilin da yasa na sanya sunan Mahaifiya ta a cikin suna na
___________________________________

Back to top button