LawShehu Rahinat Na'Allah

Menene ya halasta ka fada dangane da addinin wani ko aqidar shi, menene kuma ya haramta a hukumance?

Marubuci: Shehu Rahinat Na’Allah


Gabatarwa:


Kamar yadda muka sani Nigeria tana cikin Kasashen da ake kira da “Secular State” wato Kasashen da babu ruwan su da addini, ko kuma wadanda basu hada harkokin Siyasar Kasar da harkokin addinai ko aqidu ba, kamar yadda wani Malamin Jami’a Barr. O. E. Nwebo, Mawallafin Littafin “The Legal Implication of the Declaration of Sharia as a State Religion in Nigeria” ya fada.

Domin tabbatar da cewa Nigeria “Secular State” ne mu duba Kundin tsarin Mulkin Nigeria zamuga Babi Na 1, Sashi Na 10 yace: “Haramun ne ga gwamnatin tarayya ko gwamnatocin Jahohi su ayyana wani addini a matsayin addinin wannan Kasar, ko Jahar”

Hakanan Babi Na 4, Sashi Na 38, karamin Sashi Na 2 yace: “Haramun ne idan zaka Shiga wata Makaranta ace dole sai ka karbi wani addini (Musulunci ko kiristanci) ko ace dole sai ka rika halartar wasu activities na addinin da ba naka ba, ba na iyayen ka ba.

Dalilin da yasa Nigeria tayi wadannan dokokin shine: lura da cewa ita kasa ne data tara mabiya addinai daban-daban, dan haka ba zai yuwu ace dole ga addinin da kowa zai rika yi ba, idan kuwa ya zama haka to dole kuma ayi dokoki da zasu kula da kuma kare mutunci da hakkin mabiya kowanne addini da aqida ta bangaren maganganu ko ra’ayoyin da za’a fada a kan su, domin a samu kwanciyar hankali, yalwar arziki da zama lafiya da juna a cikin aminci.


‘YANCIN FADAR ALBARKACIN BAKI TSAKANIN ADDINAI KO AQIDU:


‘Yancin fadar albarkacin baki tsakanin addinai ko Aqidu abune da yake Very Sensitive, saboda idan ba’ayi taka tsan-tsan ba zai iya haifar da Breach of Peace a kasa, domin kuwa duk lokacin da Mabiyin wani addini ko Aqida ya zagi ko yaci zarafin wani addinin ko aqidar to akwai yuwuwar barkewar rigima, (Kowa yasan abunda ya faru lokacin zaben Sarauniyar Kyau da akayi a Mulkin Obasanjo) su kuma Shugabanni abunda basa so kenan, wato barkewar rigama.
To saboda haka dokar Nigeria bata yarda kowa ya zagi ko Ya raina, ko yaci mutuncin wasu addinai ko Aqidu ba, ko ya aibata su, idan yayi haka Zai fuskanci hukuncin dauri gidan Kaso (Prison) Na tsawon Shekara 2, kamar yadda yazo a Criminal Code, Babi Na 19, Sashi Na 204.
Haka ma yazo a Sashi Na 210, 211, 212 da 213 na Penal Code cewa: “Ba’a yarda ka zagi, ko aibata ko kaci zarafin wani addini ba ko ka raina shi ta kowanne fuska ba, haka ba’a yarda ka fadi wata magana da zata taba zuciyoyin wasu mabiya addini ko aqida ba, idan har kayi haka ka saba ma dokar kasa, za’a daure ka na tsawon Shekara biyu, idan alkali yaga dama har da tara (Fine)” shima Penal Code Na Jihar Jigawa Sashi Na 210 ya tabbatar da haka.

Dan haka ko a Islamic Law ma an haramta ka zagi/ci mutuncin addini ko aqidar wani, Allah SWT yace:
”ولاتسبوا الذين يدعون من دون الله فيسبوا الله عدوا بغير علم“

FASSARA:
“Kar Ku zagi wadanda suke bautawa wanin Allah (idan kukayi haka) sai su Kuma su rika zagin Allah………”

AKARSHE:
Duk wata magana da zakayi, duk wani karatu Ko Majlisi da Malami zaiyi to dole ne ya kiyaye harshen sa akan duk wata Aqida ko addini dangane da wadannan abubuwa:
1• Kar ya zagi kowanne addini ko Aqida
2• Kar yaci Mutuncin kowanne Addini ko Aqida
3• Kar ya raina Malaman kowanne addini ko ta’alim din su, saboda hakan zai iya haifar da Breach of Peace
4• Kar ya fadi wata maganar da ya tabbatar zata taba zuciyoyin mabiya wani addinin ko Aqidar
5• Kar ya rika yin kalaman da zasu tunzura wasu Mabiya addinan ko Aqidar.
6• Kar ya rika aibata kowace Aqida ko Addini (babu ruwan shi dasu)

Duka wadannan laifuka ne da suka saba da dokokkin kasa da ya kamata mu kiyaye.
Allah Ubangiji yayi mana Jagora, Amin.

See also  Ɗaurin Shekara 3 ne hukuncin duk wanda ya doki Matar shi

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button