Abubuwan Dake Kashe Maza A Lokacin Jima’i
An jima ana samun hadarin mutuwan maza akan mata a lokacin da suke jima’i. Tarihi ya kawo manyan mutane maza da yawa da suka mutu akan mata.
Mutumin da tarihi ya nuna shine ya soma mutuwa akan mace shine shugaban cocin Katolika na wancan lokacin mai suna Pope John XII ance ya mutu ne akan abokiyar zinarsa. Manyan mutanen irinsu Attila, Pope Leo VIII, Lord Palmerston, Prime Minister na Burtaniya a wancan lokacin shima ya mutune akan mace. Sai tsohon shugaban kasan Faransa da ya mutu a lokacin da karuwarsa take tsotson azzakarin mai suna. FĂ©lix Faure,wanda yayi rayuwa daga 1895 zuwa 1899.
Wadannan da wasu da daman gaske sun mutu akan mata a yayi gudanar da jima’i. Wanda tarihi bai kawo mace ko guda ba da aka samu wannan hadarin akanta.
Mutane da dama da zaran sunji namiji ya mace akan mace abunda ke zuwa musu a rai shine Dadin jima’in ne ya kashe shi. Haka ne, amma kashi 80 cikin dari na mutanen dake mutuwa akan mata ba dadin Jima’i bane. Akwai manyan dalilan dakan iya kashe maza a lokacin da suke gudanar da jima’i kamar hakan.
Shan Miyagun Kwayoyi- Da akwai wasu maza da suke yawan shan miyagun kwayoyi da fodar koken. Wadannan abubuwan biyu da zaran sunyi yawa a lokacinda mutun ya shasu, suna kara gudanar jini fiye da yadda ya kamata jinin dan adam ya gudana a jikinsa. Wanda haka na iya taba zuciyarsu sai daga nan numfashi ya dauke.
Yawan shan miyagun kwayoyi da koken kadai ko babu jima’i suna kashe mutum, bare kuma a kara da shi.
Shan Magungunan Kara Kuzari- Magungunan kara kuzarrin jima’i ga maza suma suna taimakawa sosai wajen mutuwan maza a yayin jima’i.
Wasu mazan sunada cutuntulan da shan wadannan kwayoyin hadarine a rayuwansu, amma suke sha wanda hakan yake zuwa ya tayar da wannan cutar a lokacinda namiji yake kan mace wanda hakan sai yayi sanadiyar mutuwarsa akan mace.
Fargaba- Akasarin wadanda suke mutuwa a lokacin jima’i tarihi ya nuna ba da matansu suke jima’in ba. Mafiya yawansu da karuwansu suke wannan harkar, kuma mutanene da ake ganin mutuncinsu. Wannan yasa a lokutan da suke jima’i basa samun natsuwa da kwanciyar hankali, wanda hakan yake shafar bugun zuciyarsu harma yayi sanadiyar mutuwarsu.
Shauki- Akwai wadanda sabar shauki da jin dadin jima’i ke sasu har numfashinsu ya dauke daga nan sari su mutu. Wanda tsoro ma yakan iya sa mutu ya samu irin hakan idan yazo da kara kwana sai mutuwa.
Wadannan sune kadan daga binciken danayi akan dalilan dake kashe maza a lokacinda suke kan mata suna gudanar da jima’i. Sai dai manyan dalilan sune shan miyagun kwayoyin da kuma shan magungunan kara kujari ga masu cututtuka irinsu hawan jini, ciwon siga da sauransu suke yi. Don haka maza sai a kiyaye.