Tambayoyi a Musulunci

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYI DA MAZIYYI DA KUMA WADIYYI


Tambaya
Assalamu alaikum.
Don Allah malam ina so a bambance min tsakanin wadannan ruwaye, wato maniyyi da maziyyi da wadiyyi, saboda nima tambaya ka yi min akan haka!

Amsa
Wa alaikum assalam
To ‘yar’uwa Allah ya datar da ke, ga abin da ya sawwaka:

1. Maniyyi Maniyyin namiji : ruwa ne mai kauri FARI wanda yake fitowa ya yin babbar sha’awa kamar saduwa, ko wasa da farji, sannan yana tunkudo juna lokacin da yake fitowa, kuma warinsa yana kama da warin hudar dabino, ko damammen gari, Idan ya bushe kuma yana yin kamshi kwai. Maniyyin mace : ruwa ne tsinkakke, MAI FATSI-FATSI, WANI LOKACIN KUMA YANA ZUWA FARI, wanda yake fitowa ya yin babbar sha’awa kamar saduwa, ko wasa da farji, sannan yana tunkudo juna lokacin da yake fitowa, sannan za ta ji tsananin sha’awa da kuma dadi lokacin da ya fito, kuma warinsa yana kama da warin hudar dabino ko damammen gari, Idan ya bushe kuma yana yin kamshi kwai, kuma za ta ji sha’awarta ta yanke bayan fitowarsa. HUKUNCINSA SHI NE : YANA WAJABTA WANKA.

2. Maziyyi : Ruwa ne tsinkakke da yake fitowa, yayin karamar sha’awa, kamar tunanin aure ko kuma tuna wacce kake so, ko matarka, ko kallon matar ko namijin da kike sha’awa, haka nan yana fitowa yayin wasa tsakanin miji da mata, saidai shi ba ya sa sha’awa ta tafi, kuma wani lokacin ba’a sanin ya fito. Malamai suna cewa : Maziyyi ya fi fitowa mata, fiye da maza, lokacin da maziyyi zai fitowa namiji azzakarinsa zai mike. HUKUNCINSA SHI NE A WANKE FARJI GABA DAYA, DA KUMA INDA YA SHAFA, KUMA A SAKE ALWALA.

3. Wadiyyi wani ruwa ne mai kauri da yake fitowa a karshen fitsari, ko kuma karshen bahaya ga wanda ya jima bai yi ba, yana fitowa ga wadanda suke fama da gwauranci ko wadanda suka yi nisa da abokin rayuwarsu ta aure, ina nufin namiji ko mace.

YANA DAUKAR DUKA HUKUNCE- HUKUNCEN FITSARI.

Allah ne mafi sani

Dr. Jamilu Zarewa

See also  ZAN IYA SADUWA DA MAI HAILA, IDAN NA SANYA CONDOM ?

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button